PDP TA NEMI GOYON BAYAN SAURAN 'YANTAKARA DON KAWAR DA GWAMNATIN APC

PDP TA NEMI GOYON BAYAN SAURAN 'YANTAKARA  DON KAWAR DA GWAMNATIN APC
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
A ranar Talatar nan 4 ga watan Janairu na 2023 jam' iyar adawa ta PDP ta Æ™addamar da yaÆ™in neman zaÉ“en É—antakarar muÆ™amin kujerar Gwamnan Jahar Katsina Sanata Yakubu Lado ÆŠanmarke a filin Aya dake cikin garin Funtuwa. Wannan taron buÉ—e gangamin yaÆ™in neman zaÉ“en ya samu halartar É—inbin magoya bayan jam'iyar.  
A wajaban shugaban jam'iyar na Jaha Alhaji Lawal Magaji Ɗan Bachi, yayi kira ga jama'ar jahar Katsina da su fito ƙwansu da kwarkwata a ranar zaɓe su zabi jam'iyar ta PDP domin fidda jama'ar jahar da ƙasa baki ɗaya daga cikin halin ƙuncin da suke ciki wanda ya zargi jam'iya mai mulki ta APC ta jefa al'ummar.
Shugaban jam'iyar har ila yau, yace, zasu cigaba da lallashin jama'a don samun goyon bayan su don ganin sunyi awon gaba da gwamnatin APC. Daga nan sai yayi kira ga sauran 'yantakarkari da su goyi bayan PDP domin ganin ta kawar da gwamnatin ta APC daga mulki a zaben na 2023, kuma tun daga ƙasa har sama.
Shi kuwa shugaban kwamitin yaÆ™in neman zaÉ“en Atiku/Lado na Jahar Katsina, Sanata Umar Tsauri jan hankalin masu yunÆ™urin tayar da husuma yayi tun daga lokacin yaÆ™in neman zaben har zuwa ga lokacin aiwatar da zaÉ“uÉ“ukan da za'ayi. Sanatan wanda ya baiyana 'ya'yan jam' iyar da cewa masu bin doka da oda ne tare da yin É—a'a, don haka yake Æ™ara jan hankalin su da kada su bari waÉ—ancan abubuwa da aka san su da su ku kubce. Sanatan ya Æ™ara tabbatarwa da jama'ar da suka halarci wannan taro da cewa, dukkan alamu sun nuna cewa jam'iyyar PDP zata yi nasara akan zaben da za'ayi. 
A nashi sashen, Babban Daraktan yaƙin neman zaɓen Atiku/Lado na Jahar Katsina kuma tsohon Sakataren gwamnatin Jahar Katsina Dokta Mustafa Inuwa, shaidawa al'ummar jahar Katsina yayi akan cewa, zaɓen Sanata Yakubu Lado a matsayin Gwamnan Jahar Katsina mafi alheri ga jama'a. A cewar shi, Sanata Lado mutun ne mai tausayi da riƙon amana, sannan ga shi da kishin al'ummarsa wajen ganin sun cigaba. Dokta ya ƙara cewa, idan har jama'ar jahar suka zaɓe shi, zasu san cewa lallai sun zabi mutumin kirki wanda zai rike amanar su saɓanin yadda aka yi masu a jam'iyar dake ci. Kazalika, zasu san cewa, sun zaɓi mutumin kirki mai son cigaban jahar wanda kuma zai kawo mata cigaban ta fuskoki daban-daban muddin aka zaɓe shi ya hau kujerar Gwamnan.
Ɗantakarar kujerar Gwamnan Jahar ta Katsina a ƙarƙashin tutar PDP Sanata Yakubu Lado a jjawabin shi, tunasar da al'ummar Jahar Katsina yayi akan irin halin ƙuncin da ake ciki. Don haka, ya tabbatarwa da jama'ar Jahar cewa, muddin suka bashi wannan dama, lallai zasu ga cigaba ta fuskokin da suka shafi maganar tsaro, ilmi, kiwon lafiya, aikin gona da sauran su. Ɗantakarar ya nemi goyon bayan jama'ar Jahar da kuma neman kuru'un su a ranar zaɓen don bashi damar hawa kujerar Gwamnan.
Daga cikin manyan jam'iyar da suka halarci wannan taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen Atiku/Lado a garin na Funtuwa sun haɗa da Sanata Ahmad Babba Kaita, Tsohon Mataimakin Gwamna a lokacin mulkin Shema Barista Sujara Umar Damari, Tsohon Shugaban jam'iyar Kabir Maiwada Daudawa. Sauran sun hada da Ajiyan Katsina Alhaji Lamis Dikko tare da shugaban matasan jam'iyar na ƙasa Alhaji Mohammad Kadade

Post a Comment

Previous Post Next Post