Nazari - KO ME ZIYARAR YAƘIN NEMAN ZABEN DIKKO RADDA TA NUNA A KANANAN HUKUMOMIN DAKE FUSKANTAR MATSALAR TSARO?
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Tabbas kowane dantakarar siyasa yana da gurin ganin ya shiga lungu da sako don ganin ya ziyarci jama'a domin samun goyon bayan su. To saidai a zaben 2023 'yan takarar na fuskantar wani babban ƙalubale kusan a wasu sassa da dama acikin fadin ƙasar baki ɗaya musamman akan abin da ya shafi sha'nin tsaro. Wasu ma daga cikin su sukan soke kai ziyarar baki ɗayanta a wasu sassan saboda fargaba.
To saidai a Jahar Katsina wadda ke ɗaya daga cikin jihohin dake fuskantar matsalar tsaron, ɗan takarar kujerar Gwamna ƙarƙashin tutar jam'iyar APC Dokta Dikko Radda ya kafa wani tarihi a wajen kai ziyarar neman goyon bayan jama'a a irin wannan hali na fargabar tsaron. Abu na farko da ya ba jama'a da dama mamaki tare da yiwa juna tambaya gami da bayar da amsa a tsakani shi ne, buɗe yaƙin neman zaɓen shi a ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da wannan matsalar tsaro ta yiwa katutu, wato, ƙaramar hukumar Faskari wadda ta zamo wadda tafi saura fuskantar wannan matsala. Acikin ƙaramar hukumar ne a tarihi mahara masu garkuwa da mutane gami da kisan ba gaira suka kaiwa garin Kadisau hari da babura 450, kowane babur kuma dauke da mutun 3 kowa da bindigar shi, ƙarƙashin jagorancin shaharren ɗan bindigar nan mai suna Adamu Aleru wanda har gobe jami'an 'yansanda da gwamnatin jahar Katsina ke neman shi.
Wannan taron buɗe yaƙin neman zaɓen a wannan yanki ya sanya guyawun wasu 'yan siyasar yin sanyi musamman daga ɓangaren 'yan-adawa da suke ta ƙoƙarin yin kamfe da wannan matsala ta tsaro wadda suke aza alhakin akan ita gwamnatin APC mai ci. Babban abin da ya fi bayar da mamakin shi ne, taruwar jama'a da yawaitar ababen hawa wanda garin Faskarin yayi kadan ga ɗaukar waɗannan abubuwa biyu, saida ta kai duk wata hanyar dake shiga garin sai da suka cika da ababen hawa a ƙalla na tsawon kilo mita ko fiye da haka, ciki kuwa har da hanyar dake zuwa Jahar Zamfara inda mafi yawa daga wannan sashen suke fitowa. Batun ganin wata alamar tsoro daga fuskokin mahalarta taron babu, hasalima, anyi zaton wani taron ɗaurin aure ne wanda shine aka fi ganin annushuwa a fuskokin angunan.
Wannan taron bude yaƙin neman zaben ya aza ɗan ba ne ga jama'a na nuni da cewa, lallai wannan ɗan takara yana da wasu abubuwa na daban wanda yake da wuyar fassarawa. Wasu na cewa, lallai akwai alamun karbar addu'ar da Dikko Radda ke yi na cewa, in alheri ne shi ga al'ummar Jahar Katsina akan neman wannan kujera, Allah ya bashi. "Mu wannan magana kowane lokaci ita muke kallon wannan yawon neman ƙuri'a da Radda ke yi. Don irin yadda ake fadin wuraren da ake shiga don neman jama'a abin yana bamu mamaki. A shiga lafiya kuma a fito lafiya duk kuwa da fargabar da ake cusawa a tsakanin jama'a, inji wani da muka zanta da shi akan wannan ziyarar neman goyon bayan da wasu ke ganin tamkar daukar Dala ne babu gammo.
Anyi zaton a wannan shiyya ta Funtuwa za'a cigaba da wannan zagaye, kwatsam, sai aka ji an nufi shiyyar Daura inda aka cigaba da zagayen ƙananan hukumomin har sai da aka kammala su. Fitowa daga can sashen, sai aka tunkaro shiyyar Katsina, nan ma sai aka fara daga karamar Kaita, daga nan sai aka nufi Jibiya, wadda ita ma tana daga cikin ƙananan hukumomin dake fuskanta wannan barazana ta tsaro. Ganau sun ce, kusan in baya ga taron Faskari, babu inda aka sake samun taruwar jama'a kamar yadda aka samu a garin na Jibiya. Wannan ma ya ƙara sa wasu alamu ga jama'a. Shin wannan Dikkon me yake taƙama da shi ne? Anya magajin Dikkon da ake cewa ba haka lamarin yake ba? Wadanda suka san tarihin Sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Dikko suna cewa, a lokacin rayuwar shi haka ya rika yi. Duk wani wurin da ya gagara ko ake jin tsoron zuwa, sai dai a ga sarki Dikko. A kuma haka ya riƙa shawo kan matsalolin da jama'ar wannan lokaci. Ɗaya daga cikin su shi ne samuwar kafa kasuwar Sabuwa daga ɓangaren Gwari da suka hana jama'ar yankin cin kasuwar da suke da ita. Yau ga kasuwa an wayi gari ta koma ƙaramar hukuma sanadiyar cigaban da Sarki Dikko ya kawo a yankin da ake fuskantar matsalar tsaron.
Tawagar ta yaƙin neman zaben ɗan takarar Gwamnan ƙarƙashin tutar APC wadda Dikko Radda ke yi, har ila yau, ta shiga yankuna mafi munin hadari, wato, ƙananan hukumomin Batsari, Ɗanmusa da Safana, kuma ta shiga har cikin wasu lunguna na ƙananan hukumomin, in baya ga wani yanki na ƙaramar hukumar Safana inda aka tafi da Magaji Umbadau, shi ma cikin ƙaramin lokaci aka sako shi. Kamar yadda wata majiya ta shaida mana, wannan ɗaukar ta Magajin anyi ta ne bisa kuskure yayin da wasu ke cewa, an shirya yin hakan ne don a kawo nakasu ga tafiyar Dikkon.
Abin lura - Akwai wasu abubuwan lura a tafiyar Dikkon a waɗannan wurare kamar haka:
i. Neman sanin irin matsalolin da ake fuskanta a waɗannan wurare daga bakunan waɗanda abin ya shafa ba wane ya ji ga wane ba.
ii. Ganewa ido irin halin da jama'ar suke ciki a zihiri don sanin abin da ya kamata ayi masu in Allah ya bashi wannan kujera.
iii. Tabbatarwa da jama'a cewar, yana tare da su acikin kowane hali suke, kuma zai iya zuwa inda suke ba tare da wani shamaki ba
iv. Ƙoƙarin ɗunke duk wata ɓaraka a tsakanin al'ummar jahar don zama uwa ɗaya uba ɗaya
v. Kawar da duk wani shakku na cika alkawalin da ya dauka muddin ya zama Gwamna musamman batun sha'anin tsaro kamar yadda ya sha fadi.
vi. Nunawa a fili a matsayin shi na matashi cewar zai iya tunkarar duk wani kalubale don kawo cigaba a jahar, domin a baiyane take cewa, wasu 'yantakarar sai wayar salula suke amfani da ita a wajen isar da sako.
Waɗannan kadan ne daga cikin nazarin da wannan kafa ta ASKGLOC NEWS tayi dangane da wancan babban ƙalubale na shiga yankunan da ake fama da matsalar tsaro da dantakarar kujerar Gwamnan Jahar Katsina Dokta Dikko Radda yayi na neman jama'ar Jahar su goya mashi baya don ganin yayi nasara a zaben 2023. Kazalika, duk inda dantakarar ya shiga kamar yadda rahotanni ke iske mana, babu inda aka samu wata matsala kafin da kuma bayan barowar shi a wannan yanki, hasalima, labaran da muke samu shi ne, wannan matsalar a kullum raguwa take yi.