In aka zabe ta - JAM'IYAR NNPP ZA TA SAMAR DA KUDIN SHIGA TA AMFANI DA HASKEN RANA A JAHAR KATSINA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
A ci gaba da yakin neman Zabe da jam'iyu ke yi a Jahar Katsina, a ranar Alhamis 5 ga watan Janairu 2023 NNPP mai kayan Marmari ta ƙaddamar da yaƙin zaben kujerar Gwamnan jahar a garin Mashi wanda Injiniya Nura Khalil ke nema. Taron ya samu halarcin dimbin magoya bayan jam'iyar daga sassa daban daban na Jahar tare kuma da kawo baici daga makwabciya jahar Kano.
A jawabin shugaban jam'iyar na jaha Alhaji Sani Liti 'Yankwani a wajen taron, yace, jama' a su hankalta akan irin halin da ake ciki na satar jama'a, kisa da sauran su wanda rashin ilmi, da sauran matsalolin da har yau gwamnatin dake ciki bata kula akan su ba. Akan haka yayi kira ga a zabi jam'iyar su ta NNPP wadda yace, zata kawo karshen duk wadannan matsalolin da ake fuskanta musamman na rashin tsaro da makamantan haka. Shugaban jam'iyar yayi bayani mai tsawo duk da cewar da yayi ba lokacin yin lacca ba ne.
Shugaban jam'iyar kuma dan takarar shugaban kasa Dokta Rabi'u Musa Kwankwaso wanda ya samu wakilcin dan takarar kujerar Gwamna a jahar Kano a karkashin jam'iyar, Alhaji Abba Yusuf wanda aka fi sani da Abba gida-gida yace, akwai kyakyawar alaka da kawance a tsakanin jihohin biyu akan haka ne suka zo wajen bikin kaddamar da yakin neman zaben kujerar Gwamna a jahar ta Katsina, duk da cewa, yana wakiltar shugaban jam'iyar na ƙasa ne. Abba gida-gida ya kara da cewa, lallai jama'a su fito su zabi jam'iyar NNPP kuma sannan su sa ido tare da kare kuri'un su duk da cewa a wannan karon yin magudin zabe ko satar akwati da sauran irin su zaiyi wuya bisa ga irin shirin da ita hukumar zabe mai zaman kanta tayi tanadi mai kyau. Ya kara da cewa, har in aka zabi NNPP to akwai tanade-tanaden da tayi bama kamar ga mata da matasa na samar masu da aiyun yi da kuma tallafin sana'o'i, kawo karshen matsalar tsaro da kuma kare addinin musulunci. Kazalika, zasu rike amanar jama'a.
Shi kuma dan takarar kujerar Gwamnan Jahar Katsina Injiniya Nura Khalil, cewa yayi, azzalumar gwamnatin dake bisa gado yanzu wadda suke fata turewa, ta kwashe komi a jahar ta Katsina. Sannan ya ce, "ana bin mata ana sayen katunan zaben su akan naira dubu goma amma kuma akarshe sai a basu dari biyar, to a sani babu batun magudi a wannan zaben balle a ba wani katin wani yaje ya jefa kuri'a sama da goma". Dan takarar ya baiyana jahar ta Katsina a matsayin jahar da tafi saura hadari saboda rashin tsaro, inda yace jam'iyar su ta NNPP muddin ta hau mulki zata kawar da duk wadannan matsaloli, don haka yake kira ga al'ummar Jahar Katsina da su fito su zabe su don kawo cigaba.
Injiniya Nura dantakarar kujerar Gwamnan jahar Katsina ya baiyana dalilin shi na zabar karamar hukumar Mashi don kaddamar da yakin neman zaben shi. "Na fara da Mashi ne saboda da ita da Daurawa ta Jahar Jigawa da Kankiya bisa ga binciken da muka yi sun fi samar da hasken rana wadda zata samar da hasken wutar lantarki ba sai an jira daga wani wuri ba. Har ila yau, samu yi amfani da wannan hasken wutar lantarkin don samawa jahar kudaden shigar da akalla za'a samu naira bilyan 100 acikin shekara ta wannan fuskar. Kudaden zamu yi amfani da su wajen gudanar da aiyukan gwamnati ba sai mun jira na gwamnatin tarayya ba. Har ila yau, muna da shirin kafa banki mallakar gwamnatin jahar wanda har zai iya bayar da damar yin ajiya mai kama da shirin adashe don dai mu farfado da tattalin arzikin jahar muddin kuka zabe mu a wannan zabe na 2023".
Dantakarar kujerar Gwamnan ya kuma zargi gwamnatin APC ta jahar Katsina akan yiwa fannin ilmi rikon sakainar kashi, inda yace acikin shekaru 7 da gwamnatin tayi a bisa mulki, yara dubu 100 ne basu jarabawa ba. Don haka ya kara yin kira ga jama'a da su fito ranar zaben don su kadawa jam'iyar NNPP mai alamar kayan marmari kuri'un su don ganin an fita daga cikin kuncin da rashin tsaron da al'umma suke ciki.