HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA NA CIGABA DA BIYAN RARAR KUDIN AIKIN HAJJ NA 2021/22

HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA NA CI GABA DA BIYAN RARAR KUDIN AIKIN HAJJ NA 2021/22

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 

Hukumar jin dadin alhazai ta Jahar Katsina na ci gaba da biyan sauran rarar kudaden aikin Hajj na 2021 da 2022 ga mahajjatan da suka yi aikin Hajjin na 2022 wadanda kuma suka zuba kudin aikin har naira milyan biyu da rabi da suka shafi har da na guzuri, ana kira ga mahajjatan da su gaggauta bayar da lambobin asusun ajiyar su na banki ko na amintattun su domin karbar ragowar tsabar kudin su har naira dubu 50 da 392 da kobo 11. 
  
Kamar yadda sanarwar da jami'in hulda da jama'a na hukumar Alhaji Bello Badaru Karofi ya sanyawa hannu ta ce, ana yin kira ga wadanda abin ya shafa da su hanzar zuwa ofisoshin hukumar da suka biya kudaden don karin bayani. 
Indai za'a iya tuna, akwai maniyatan Jahar Katsina da basu samu damar zuwa aikin hajji na 2020 da 2021 ba, wadanda wasun su suka yi hakurin barin kudaden nasu har aka samu damar zuwa aikin na 2022 amma gami da karin kudi na naira milyan guda, kuma suka cika domin sabke wannan farali. Yayin da a hannu guda hukumar karkashin jagorancin Babban Daraktan ta Alhaji Sulemain Nuhu Kuki ta dauki tsarin wanda ya riga biya shi za'a fara baiwa kula. Hakan ne ya sa har hukumar ta samu damar aiwatar da aikin Hajjin na 2022 cikin nasara. 

Post a Comment

Previous Post Next Post