DIKKO RADDA BA ZAI BAR ILMI YA LALACE BA A JAHAR KATSINA - Shugaban NUT

DIKKO RADDA BA ZAI BAR ILMI YA LALACE BA A JAHAR KATSINA - Shugaban NUT
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
An baiyana É—an takarar kujerar Gwamnan Jahar Katsina Æ™arÆ™ashin jam'iyar APC Dokta Dikko Radda da cewa, in Allah ya bashi ikon hawa kujerar ba zai bar harkokin ilmi su lalace ba.  
 Shugaban Æ™ungiyar Malamai NUT na Jahar Katsina Alhaji Abdullahi Falalu Mai'adua ÆŠankafin Daura ya baiyana haka a wajen taron da tsaffin É—aliban makarantar horas da malamai ta gwamnatin tarayya dake Kafacan suka gudanar a ranar lahadin da ta gabata a dakin taro na ERC dake cikin garin Katsina domin baiyana goyon bayan su ga tsohon daliban makarantar wadanda ke takarar kujerun Gwamna da Mataimakin shi, wato, Radda/Jobe 2023.
Shugaban ƙungiyar malaman wanda ya ce, a iya sanin shi da Radda wanda yake ya taba yin malanta bayan shugabancin karamar hukumar Charanci har ta kai ga lokacin da ya rike shugaban ma'aikata na gidan gwamnatin jahar Katsina, bai taba ganin lokacin da wani malami ko kungiyar ta malamai wanda yaje neman wani abu a wajen shi ya taras da kofar shi a rufe. "Idan zamu tuna baya, a lokacin marigayi shugaban kasa Umaru 'Yar'aduwa yana Gwamnan Jahar Katsina wanda shine ya fara yiwa makarantun mu na firamare bene, a matakin karamar hukuma, Dikko Radda ne wanda yayi bene a garin Charanci. Ko wannan kadai ya isa mu gane cewa, mutun ne wanda ke kula da harkokin ilmi kamar yadda Gwamna Masari ya ke yi. A yanzu, in baya ga karin girma na 2022 da muke jira, babu wani abin da malaman makaranta zasu ce suna bin wannan gwamnati ta Mai girma Gwamna Masari. Batun kayan aiki da kula da makarantun hatta da daliban babu abin da zamu cewa wannan gwamnatin ta Masari sai godiya. To bisa ga wannan kyakkyawar hanya da Gwamna Masari ya bi ta fuskar ilmi, haka muke kyautata zaton in Allah ya bada Dikko wannan kujera zai dora harma ya wuce inda ba'a zato a wajen ciyar da ilmin gaba".
Shi dai wannan taron kungiyar shi ne karo na uku wanda aka yi a shiryar Katsina Æ™arÆ™ashin jagoranci Alhaji Isma'ila Kofar Sauri wanda kuma shi ne shugaban makarantar Je-ka-ka dawo dake Kofar Yandaka acikin garin Katsina. Taron har ila yau, ya samu hakartar babban jami'in tuntuba na kungiyar Alhaji Umar Dangi Abbas da sauran jagororin kungiyar daga sassa daban-daban aciki da wajen jahar. 

1 Comments

  1. Yanzu kaji wani yace ai biyan ka akayi kayi wannan maganar, ita dai gaskiya daya ce kuma shi yasa tarihi yake da amfani in banda matuwa ta shiga duhun kai na wasu tama ya zaka hada ladodo da Dr Dikko Umar Radda PhD da wani secondary drop out chan.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post