Da dumi dumi - PDP TA YI KAMUN MUTUN 9390 DAGA APC A KARAMAR HUKUMAR KURFI

Da dumi dumi - PDP TA YI KAMUN MUTUN 9390 DAGA APC A KARAMAR HUKUMAR KURFI 

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 

A wajen taron yaÆ™in neman zaben jam'iyar PDP a karamar hukumar Kurfi, shugaban kwamitin yakin neman zaben, tsohon Sakataren jam'iyar na kasa kuma tsohon Sanata Umar Tsauri ya sanar da cewa, jam'iyar tayi nasarar samun mutanen da suka yi canjin sheka daga jam'iyar APC zuwa PDP har mutane 9390 daga hannun mutane biyu na jam'iyar ta APC wato,  Bishir Lawal wanda ya zo da mutane 6373 yayin da Dahiru Maradi wanda aka fi sani da Baba Dahe ya zo da mutane 3013.
Wannan na daga cikin irin manyan nasarorin da jam' iyar ke samu a duk inda suka je, wanda matsin rayuwa ke sanya jama'a na yin wannan canjin sheka. 

Post a Comment

Previous Post Next Post