AN YABAWA HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA KAN YADDA TA GUDANAR DA AIKIN HAJJ NA 2022 - Jama'a

AN YABAWA HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA KAN YADDA TA GUDANAR DA AIKIN HAJJ NA 2022 - Jama'a
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
   

Al-umma a Jahar Katsina musamman wadanda suka gudanar da aikin Hajji na 2022 sun yabawa hukumar jin dadin Alhazai ta jahar bisa ga irin yadda suka gudanar da aikin hajjin na 2022. Wani mahajjati mai suna Alhaji Sani Bakin Kasuwa yace, "aikin hajjin 2022 shi ne aikina na 12 banda zuwa Umra, amma babu wanda naji dadin shi kamar wannan da naje. Farko dai a tarihi, shi ne zance na samu masabki kusa da Harami, kuma na zauna tare da su jami'an wannan hukuma wanda ko tari mutun yayi mai karfi sai sun fito sun yi tambayar abinda ya faru. Na shekarar 2019 ne wanda shi ma ba zan manta da shi ba. Duk da cewa wanda yayi Amirul Hajj na wannan shekara Alhaji Muntari Lawal ba da shi aka shirya aikin ba tun farko, amma irin yadda ya tsaya ganin cewa, mahajjatan jahar Katsina basu shiga cikin wani yanayi ba. Gaskiya nan ma anyi kokari. Sau da yawa in na dawo masabki ko dai in taras da shi bakin kofa gidan mu zaune ko ace yanzu ya bar nan. Irin halin ko in kula da aka rika yi mana a baya gaskiyar magana a lokacin shi wannan abu bai faru ba. Ya ba marada kunya, tunda farko ance wai baya iyawa. Sai gashi ya sa tun daga lokacin shi jahar Katsina ta fara maido da sunanta akan aikin Hajjin. Ai muna da labarin har karrama mashi aka yi acan hedkwatar ƙasa.
A wata hira ta waya da wakilin ASKGLOC NEWS yayi da wani daga Funtuwa, duk da yace, a sakaya sunan shi cewa yayi, "wato, ni abinda ba zan manta da shi ba, kuma abinda zance ba'a taba yi a wannan hukuma tun kirkiro ta shi ne, ace gobe ko jibi ake rufe filin jirgi a Saudiya, amma ace jami'an hukumar sun tafi hedkwatar hukumar dake Abuja domin ganin sun nemowa maniyatansu hakkinsu da ya sagale musamman Biza. Wannan abu ya dade yana bani mamaki. Maimakon su tafi abin su kamar yadda wasu ke yi, amma suka tsaya lallai sai da suka tabbatar babu wani wanda ya biya kudin shi da bai samu tafiya ba. Duk da banje ba, amma duk wani kokkari da kuma matsalolin da wadannan jami'ai suka fuskanta muna da labari. Babbar addu'ar mu dai gare su shi ne Allah yayi masu sakayya da alheri".
Ita kuwa Hajiya Jummai roko ne tayi ga hukumar musamman akan abinda ya shafi sashen mata. "Muna ganin kokarin da jami'an suke yi anan gida da kuma can kasa mai tsarki musamman a lokacin tashi da kuma sabkar jirgi. To amma wani abin da na lura da shi shine, anan gida za'a jami'an hukumar nan mata a filin jirgi domin kula da mata, amma in anje filin jirgi na Jidda ko Madina, babu wata jami'a mace a wajen tarbar alhazai. Komi maza ke yi. Shin hukumomin ne acan ke basu bari ko kuwa matan ne ke basu son yi. Don haka nike rokon wannan hukuma ta tamu ta Katsina da ta dubi wannan lamari. Ance ciwon mace na mace ne. Irin yadda matan ke kokari a wajen daukar maniyata a jirgi, yana da kyau a can ma a samu mata masu tarbar. Wasu matan basu taba shiga jirgin ba, komi na iya faruwa a lokacin da zasu sabka kuma a bakon wuri.
Kashi 90 cikin 100 na wadanda aka zanta da su sun yaba da irin yadda aka gudanar da aikin na 2022. Sun kuma yi fatan sake samun abinda yafi na daga abinda suka gani a shekarar 2023 da ake cikin shirye-shiryen yi a yanzu. Babban korafin jama-ar da suka je aikin wanda kuma suke fatan a samu canji a kai shi ne, batun ma'aikatan kiwon lafiya, wanda suke ganin bai kamata ace ita NAHCO ta rike komi a kai. "A bar kowace jaha ta ji da ma'aikatan lafiyarta, domin su suka fi sanin yanayin al'ummar su. Haka ma batun abinci, domin irin abinda ya faru a 2022 akan abinci bamu fatar ya sake faruwa. Amma idan da jaha za'a sakarwa tayi abincinta da kanta, ta san irin abincin da al'ummar ta suke butaka. Saidai anan muna jinjinawa gwamnatin Jahar Katsina Æ™arÆ™ashin jagorancin Gwamna Masari akan irin yadda take tallafawa mahajjata acan Æ™asa mai tsarki musamman Riyal 300 da ake ba kowane mutun ba tare da wani bambanci ba. Kazalika, wadanda muka zanta da su sun yaba akan irin yadda suka ji cewar yanzu haka ana aikin fadada filin jirgin saman na Katsina wanda zai bayar da damar samar da mai ga jirgi da kuma wasu 'yan gyare-gyaren, sannan ga bayar da damar sabkar manyan jirage masu daukar kaya. 

Post a Comment

Previous Post Next Post