YADDA 442 YA SAMU TAKARDUN ZAMA ƊAN ƘASAR NIJAR - Bincike na musamman
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Labarai iri-iri sun yi yawo a kafafen sadarwa akan batun kamun mawaƙin nan mai suna Mubarak Abdulkarim wanda aka fi sani da sunan 442, ɗan yankin Zariya ta Jahar Kaduna a Najeriya, wanda hukumomi a ƙasar Nijer suka kama bisa tuhumarsa da yunƙurin yin fasfo na ƙasar ta hanyar yin amfani da takardun bogi na zama ɗan ƙasar.
ASKGLOCNEWS tayi bincike mai zurfi akan wannan lamari domin gano zahirin yadda lamarin ya faru har ya zamo aka kama 442 ofishin yin fasfo na ƙasar dake birnin Yamai ba wai a filin jirgin samar ƙasar ba kamar yadda wasu ke cewa.
YADDA YA SAMU TAKARDUN BOGIN - Kamar yadda majiyoyin mu masu tushe suka baiyana mana, shi dai 442 ya fara neman wadannan takardun zama ɗan ƙasar ta Nijer tun yana nan Najeriya ta yanyar wasu 'yan wasa(masu shirin fim) dake Maradi. Kamar yadda rahotan yace, 442 sun riƙa musayar bayanai tare da tura kudi ga su wadannan 'yan wasa(an sakaya sunaye) dake da alaƙa da su 442 ɗin ta fannin sana'ar su.
Rahotannin sun ce, takardun da su 442 suka nema don zama 'yan ƙasar sun hada har da na haihuwa wanda hakan na daga cikin sharuddan samun kowace irin dama a ƙasar kamar yadda tsarin dokar ƙasar da ma wasu ƙasashen suka tanada. Lallai ne a samu shaida daga wajen Mai gari, takardar asibiti da sauran irin su. Baya ga samar da takardun haihuwa don zama ɗan ƙasa, har ila yau, yin auren 'yar ƙasar na bayar da damar zama ɗan ƙasar koda babu waɗancan takardu muddin akwai takardar shaidar yin auren da kuma tabbacin Mai unguwa ko Mai gari, ko kuma ita matar koda babu ɗaya daga cikin waɗancan shaidu ba. Muddin zasu je alƙali su shaida cewar su ma'aurata ne ga kuma shaidar auren su, hakan ya ba mijin zama ɗan ƙasar nan take.
Kazalika, neman zama ɗan ƙasar ta hanyar rubutu, wato yin rejista wanda mai son yin hakan zaije kotu ya shaidawa alƙali bukatar shi bayan ya baiyana dalilan shi da suka haɗa da yawan lokacin da yake zaune acikin ƙasar, irin sana'ar da yake yi, wurin zaman shi da sauran su. Idan alkali ya gamsu da bayanan mai son zaman nan take za'a bashi iznin zama ɗan ƙasar. In kuma akwai wani abin da alkalin bai gamsu da shi ba, zai ƙara yin bincike tare da bayar da shawara ga mai bukatar.
Duk da sanin waɗannan ƙa'idoji da su wadancan 'yan ƙasar suka sani, sun yi fatali da su inda suka fi amincewa da su bi hanyar cuwa-cuwa. Binciken mu ya tabbatar da cewa, an yiwa su 442 wadannan takardu a Maradi, sai dai kuma ance daga yankin Ɗan Issa dake zaman tamkar ƙaramar hukuma a Jahar Maradin anan aka yi waɗannan takardu. Majiyar tace, wannan yanki yayi suna akan irin wannan harka ta yin takardun bogi ta fuskoki daban dabam. Abokan su 442 'yan Maradi ance sunyi amfani da wannan masaniya da ake yi don samun wadannan takardu wadanda kuma suka yi sa'ar samarwa 442 da abokin shi Ola bayan su kuma daga nan suka biya duk wani abin da aka caje su. Suka kuma kama hanya domin kaiwa ga cimma ƙudurin su na son shiga ƙasar Turai.
TA YAYA SUKA SHIGA NIJER - Kamar yadda aka sani, ana shiga kowace irin ƙasa ta hanyoyi biyu, wato, ta ƙa'ida, wato, yin amfani da takardun da aka yarda da su, ko ɓarauniyar hanya. A ƙasashen Afirka ta Yamma sun amince a tsakanin su cewa, ba lallai sai mai son yin zirga-zirga tsakanin su yayi amfani da fasgo ko fasfo ba, sai suka ɓullo da wani nau'in takardar shiga a tsakanin su wadda ake kira "ECOWAS - CEDEAO". Da wannan mutun zai shiga cikin wadannan ƙasashe na Afirka ta Yamma in banda ƙasar Ghana.
Ko da me su 442 suka yi amfani da shi domin tsallakawa zuwa cikin ƙasar ta Nijer? Shin babban fasfo, Ecowas ko ta ɓarauniyar hanyar? Idan da Ecowas suka shiga, me yasa basu nemi fasfo na Najeriya tun farko don yin amfani da shi tunda suna da wancan kuduri? In kuma da Ecowas suka shiga, menene manufarsu ta neman wancan fasko na wata ƙasa bayan akwai shi a ƙasar su? Ko kuwa sun bi ta ɓarauniyar hanya ce? Su dai jami'an shigi da fici a Najeriya musamman na Jahar Katsina wadda ita ce babbar hanyar da mai zuwa Maradi zai biyo daga kudancin Jahar sun baiyana cewa, basu da wata masaniya akan waccan bahallatsa ta su 442 tunda ba acikin ƙasar su aka yi ba, kuma ba'a kama su da wata takardar hukumar su ba.
Wannan ya nuna cewa, tuni su 442 suke da wata boyayyar manufa wadda da gurin su ya cika, to da sunayen ƙasashen biyu sun ƙara shiga cikin wani hali musamman na ɓatanci. Sannan ko za'a iya cewa, akwai sakacin jami'an tsaron kan iyakokin ƙasashen da basu yin binciken ƙwaƙwab ko kuwa suna bin abin da ya biyo ta hsnnun su ne kawai. Shin yaya ake yi har waɗanda ake azawa alhakin bayar da takardu masu muhimmanci ake samun na cuwa-cuwa acikin su? Me yasa 'yan waɗannan ƙasashen biyu musamman Najeriya da Nijer suke sha'awar takardun juna? Waɗannan tambayoyi har zuwa yau ɗin nan babu wanda zaice ga amsar su.
INA NE ASIRIN YA TONU? Bayan samun waɗannan takardun zama ɗan ƙasa da su Mubarak 442 suka samu na Nijer a kuma cikin ƙasar ta hannun 'yan ƙasar, sun tsallake duk wasu shingayen bisa hanyar dake tsakanin Jahar Maradi zuwa birnin Yamai, tafiyar a ƙalla kilomita sama da 700.
Duk da binciken takardu da jami'an ƙasar ke yi, 442 ya shammace su sun gaza gane takardun bogi ne yake ɗauke da su, ko kuma an bi irin hanyar da aka same su ne har ya kai ga shiga birnin na Yamai? To a ina ne asirin hakan ya faru, a filin sabkar jiragen saman ƙasa da ƙasa ne kamar yadda wasu ke cewa, ko kuwa akwai wani wurin daban? Wane hali mawaƙan suke cikin shi a yanzu? Shin wannan matsala ta shafi ofishin Jakadancin Najeriya ke Nijer kasancewar ɗan ƙasarta ne aka kama, ko kuwa akwai wani abin da ofishin ke shirin yi akan matsalar, wato, ɗaukar mataki ko kuma abin da masu iya magana ke cewa, 'kowa ya ɗebo da zafi bakin shi?
.... Zamu ci gaba