WADDA TA KASHE JARIRINTA TA JEFA RAMI TA SHIGA HANNU

WADDA TA KASHE JARIRINTA TA JEFA RAMI TA SHIGA HANNU 
Daga Umar Akilu Majeri Dutse
Rundunar Yansandan Jihar Jigawa ta Sami nasarar chafke wata Mata Yar kimanin shekara talatin da biyar a duniya wadda ake zargi da murde wuyan jaririn da ta haifa ba ta hanyar aure ba har ya mutu ta kuma jefa gawar a ramin masai. 
Matar mai suna  Balaraba Shehu  'yar asalin Æ™auyen Tsurma dake cikin yankin karamar hukumar  Kiyawa a Jihar Jigawa wadda ake tuhuma da laifin makure Jaririn har ya mutu kasancewar ta Sami cikinsa ta hanyar zina yanzu haka tana hannun hukumar 'yansandan Jihar suna bincike. 
'Yansanda sun ziyarci kauyen bayan samun labarin faruwar lamarin sun kuma cafko ta tare da tsare ta don yin bincike inda har ta ambaci abokin da suke shsrholiyar har aka samu cikin da ta haifa kuma ta kashe bisa shawarar shi wanda yayi mata cikin don gudun kada suyi abin kunya. 
 
Tuni dai aka tono gawar wannan jariri domin ci gaba da binciken. Har ila yau, yansanda sun yi nasarar kamo wanda ake zargin yiwa Balaraba cikin kuma ya bata waccan gurguwar shawara su halaka jaririn. Wanda ake zargin mai suna Adamu Sale mai kimanin shekaru 25 mazaunin kauyan Akar acikin yankin na qaramar hukumar ta Kiyawa yana hannun jami'an 'yansandan don ci gaba da binciken su
Kamar yadda kwamashinan yansandan Jahar Jigawa Mr Emmanual Ekot ya bayar da urmarni an miƙa matar da kuma abokin fasadin nata zuwa sahin bincike na farin kaya na Rundunar yansanda domin aiwatar da bincike akansu. Da zarar an kammala binciken za'a gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskanci hukunci akan laifin da ake tuhumarsu da aikatawa

Post a Comment

Previous Post Next Post