KOTU TA HANA HUKUMAR DSS KAMA GWAMNAN BABBAN BANKIN NIJERIYA EMEFIELE
Wata Babbar kotu a Najeriya ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a M. A. Hassan ta bayar da umarnin hana kamawa tare da tsare Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele bisa tuhumar da hukumar DSS ke yi mashi na laifin bayar da kudaden yin aiyukan ta'addanci da sauran laifuffukan da suka shafi tattalin arzikin ƙasa.
A ranar Alhamishin nan ce aka miƙawa Babban Sufeton 'Yansanda, Babban Lauyan gwamnati da kuma hukumar yiwa tattalin arzikin ƙasa tu'nnati, wato, EFCC takardar da umarnin kotu bisa jagorancin Mai Shari'a M. A. Hassan ta bayar na hana kama Gwamnan bankin Mista Emefiele.
Ita dai hukumar DSS ta gabatar da takardar ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS2255/2022 inda ta nemi umarnin kama Gwamnan Babban Bankin Mista Godwin bisa tuhumar shi da laifin aiyukan ta'addanci, zamba da kuma laifukan da suka shafi tattalin arziki, inda Babban Alkalin kotun Tarayya Mai Shari'a John Tsoho yayi watsi da wannan tuhuma tun a ranar 9 ga watan Disamba na 2022 bisa dalilin rashin kawo wata hujja cikakkiya daga DSS da zata sa su kama shi. Tun farko wata ƙungiya ce mai suna "Incorporated Trustee of Forum for Accountability and Good Leadership ta shigar da ƙarar mai lamba FCT/HC/CV/GAR/41/2022.
Alƙalin Kotun Mai Shari'a M. A. Hassan yace, hukumar ta DSS ta bi abin ba bisa ƙa'ida ba na hana Gwamnan bankin yin aikin shi na abin da ya shafi kuɗi da tattalin arzikin ƙasa. Akan haka, Mai Shari'ar ya haramtawa hukumar tare da shaida masu cewar kada su ci gaba da cin zarafi ko yunƙurin kama Gwamnan Babban Bankin Godwin Emefiele domin duk wani zargin da ake yi mashi sai da umarnin Babbar kotun. Kazalika, an baiyanawa masu shigar da ƙarar cewar basu da isassun hujjojin yin hakan, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.