AN BAIWA ALƘALAN SHARI'AR MUSULUNCI SABBIN MOTOCI A KATSINA

AN BAIWAR ALKALAN SHARI'AR MUSULUNCI SABBIN MOTOCI A KATSINA 

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 

Babbar kotun daukaka kara ta addinin Musulunci ƙarƙashin jagorancin Alƙalin alƙalai na Jahar Dokta Kabir Abubakar ta ba wasu alƙalai sabbin motoci domin tafiyar da harkokin aikin su. Alkalan da suka hada da Khadi Makiyu Adam, Khadi Salihu Yarima da kuma Khadi Kabir Hamisu Bello wanda dukkansu suka samu mota kirar Peogeot 605,sai kuma Bus wadda za'a rika hidimomin ma'aikatar.
Kamar yadda Alkalin alkalan Mai Shari'a Dokta Kabir yace, an sayawa manyan alkalan motocin ne don su kara samun natsuwa a wajen gudanar da aiyukan su acikin adalci ba tare da zullumin komi ba. Yayi fatan Allah ya ci gaba da yi masu jagoranci akan aiyukan su na shari'a akan adalci. 
  
A nashi jawabin, Babban Jojin Jahar Katsina, wanda kuma shi ne wanda ya hannanta wadannan motoci ga manyan alkalan, Mai Shari'ar Musa Danladi Abubakar ya jinjinawa wannan sashe na shari'a da yayi kokari tare da jajircewa akan sayen waɗannan motoci domin ganin cewa sun tafiyar da aikin su ba tare da tunanin wani abu ba. Kamar yadda yace, mafi yawan mutane basu sanin irin nauyin dake kan alkalai ba. Baya ga hidimomin gida, akwai na jama'a sannan kuma ga na ita kanta shari'ar. 
Babban Jojin ya ƙara da cewa, ba wadannan alkalai ababen hawan ya ƙara martaba basu tare da kara tsare matsayin su na alkalai. "Ganin alkali na hawan Ƙurƙura ko motar haya, babu mutunci aciki, domin tana iya kasancewa kodai su shiga motar tare da wani mai laifin da shi ne ke yi mashi shari'a ko wani abu makamancin haka. Amma ya zamo duk inda zai tafi yana tafiya cikin natsuwa, hakan zai bashi damar tafiyar da aikin shi cikin natsuwa. 
Da yake jawabi a madadin sauran alkalan da suka samu wadannan motoci, Khadi Salihu Yarima ya yabawa wannan Babbar kotun daukaka kara ta addinin Musulunci akan irin wannan tunani da hangen nesan da suka yi don samar da wadannan motoci gare su. Kazalika, ya yabawa gwamnatin Jahar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Masari akan irin gudummuwar da yake ba fannin shari'a. Sannan ya jinjinawa shi Babban Alkalin alkalan Dokta Kabir Abubakar da kuma shi Babban Jojin Jahar Mai Shari'a Musa Danladi Abubakar akan irin yadda suke gudanar da shugabancin da suke yi bisa adalci. 

Post a Comment

Previous Post Next Post