Al'ajabi - YA SAKI MATAR SHI SABODA TSAKANIN KYAU DA TAKE DA SHI

Al'ajabi - YA SAKI MATAR SHI SABODA TSANANIN KYAU DA TAKE DA SHI
         
Wani mutun mai suna Anorld Masuka mai shekaru 40 ɗan ƙasar Zimbabwe ya saki matar shi mai suna Hilder Mleya mai shekaru 30 a gaban mai shari'a Henry Chizvidzo a wata kotu a ƙasar. Kamar yadda Anorld ya shaidawa alƙalin, ba shi da sauran wata sha'awa akan matar saboda tsananin kyawon da Allah yayi mata wanda hakan yana hana shi barci saboda tunani da zullumi wanda hakan ke hana shi zuwa wajen aiki saboda tsoron kada ya barta a gida ita kaɗai wasu mazan su zo suyi mashi awon gaba da ita.
Bisa wannan dalili ne yaga cewa, kwanciyar hankalin shi da zaman lafiya shi ne ya sake ta kawai, kuma ya sake ta. Wannan lamarin ya É—aurewa alÆ™alin kai inda yace, bakin iya sanin shi ta fuskar shari'a bai taÉ“a samun irin wannan shari'a ba sai a wannan karon koda kuwa a labari ne. 

Post a Comment

Previous Post Next Post