Aikin Hajji 2023 - HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA JIHAR TA FARA KARBAR NAIRA MILIYAN ƊAYA DA RABI AMATSAYIN KUDIN AJIYA AKAN TSARIN FARA HIDIMA GA NA FARKON BIYA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Katsina ta fara karbar kudaden ajiyar aikin Hajjin shekarar 2023 mai zuwa daga hannun maniyyatan da za su yi aikin. A cewar sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar Alhaji Badaru Bello Karofi ya sanya wa hannu, Babban Daraktan hukumar Alhaji Suleiman Nuhu Kuki ya ce, fara karbar kudin ajiyar ya biyo bayan amincewar da Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bayar ga hukumar da zata fara shirye-shiryen aikin hajjin 2023, rijista da kuma tara kudaden ajiya a fadin Jahar.
Babban Daraktan Suleiman ya ce, mahajjatan za su biya Naira miliyan 1 da rabi a matsayin mafi karancin ajiya a wurin yin rajista, sannan su cika wani Naira miliyan 1 cikon da zai bayar da jimla Naira miliyan 2 da rabi kafin karshen watan Janairu, kuma za a biya dukkan kudaden ta hanyar daftarin banki wanda zai biya hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Katsina.
Kamar yadda ya bayyana a cikin sanarwar da PRO ya fitar, za a gudanar da rijistar kasance a ofisoshin shiyoyi bakwai na hukumar, wato, Katsina, Funtua, Malumfashi, Dutsinma, Kankia, Daura. da Mani domin kaucewa fadawa hannun bata gari. Sannan za'a cigaba da tsarin fara yin hidima ga duk wanda ya fara biya.
Alhaji Sulemain ya ci gaba da bayanin cewa Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta umurci dukkan Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohi da su fara rajistar maniyyata aikin hajjin 2023 har zuwa lokacin da za a ba da ka’idoji da kuma adadi ga Jihohi. Daga nan ne Babban Daraktan ya bukaci Alhazai da su tuntubi shiyoyin hukumar don neman ƙarin bayani.
Idan za a iya tunawa, wannan shi ne karo na biyu da hukumar za ta gudanar da ayyukan tun bayan bullar cutar Covid-19 a duk fadin duniya. Hukumar ta Jahar Katsina( PWB) a farkon fara aikin Hajjin a shekarar 2022, ta zama ta farko ta bangarori da dama da ta kai ga samun kyautuka daban-daban guda 5 gami da yabo saboda irin rawar da ta taka da ta wuce saura a lokacin aikin Hajjin na 2022.