YUNƘURIN YIN TAKARDUN BOGI YA KAI MAWAƘI 442 HANNUN JAMI'AN TSARO A NIJER
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Mawaƙin nan mai suna 442 wanda suke waƙa tare da tsohuwar zaruma acikin shirin fim mai dogon zango na Kwana tis'in wato Safara'u na can tsare a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijer bisa zargin yunƙurin yin sojan gona ta hanyar yin fasgon ƙasar da ba tashi ba domin samun damar fita ƙasashen waje.
442 tare da abokin shi kamar yadda rahoton ya iske mana, sun shiga ƙasar ta Nijer ne inda suka nemi yin fasgo na ƙasar wanda zai basu damar fita zuwa wasu ƙasashen. Sai dai abin ya zo masu da rashin sa'a, domin kafin a yiwa mutun shi sai ya kawo duk wasu takardun shedar cewa shi ɗan ƙasa ne, ciki harda batun cikakken bayanin mahaifi ko mahaifiya baya ga na mahukuntan yankin da mutun ya fito da suka haɗa da sarakunan gargajiya.
Su 442 sun samu yin waɗannan takardu. To amma inda gizo ke saƙar shi ne, can hukumomin dake yin wannan takardar ba haka nan kawai da an kai masu takardun suke yi ba, sai sun gudanar da nasu binciken na musamman don tabbatar da sahihancin takardun, kamar yadda shaidar gani da ido ga abin da ya faru kuma ɗan jarida mai suna Mitu ya shaida.
Rashin amincewa da waɗannan takardu yasa jami'an tsare 442 da abokin tafiyar shi Ola don gudanar da bincike. Saidai babu Safara'u acikin wannan lamari kamar yadda wasu ke cewa. "Yaron mu mai suna Souleiman Ramzi wanda yake mawaƙi ne anan Yamai abin ya so ya shafa. Amma su 442 sun bayar da shedar cewa, shi ya rako su wannan ofis ne kawai, kuma nan take aka sake shi. Ya zuwa rubuta wannan labarin, su 442 suna tsare kwanaki uku da suka wuce, za'a kuma tura su zuwa gaba kamar yadda dokar ƙasar ta tanada inda jami'an tsaro ke da damar tsare wanda suke tuhuma har na tsawon kwanaki uku kafin tura shi zuwa inda ya dace. Kazalika, rahoton yace, babu wata maganar kudi don bayar da su beli kamar yadda ake yaɗawa. "Suna cikin ƙoshin lafiya, babu wata alamar takura tare da su.