'YANSANDA SUN CAFKE WANI MUTUN DA LAIFIN SHIGAR MATA


'YANSANDA SUN KAMA WANI MUTUN DA LAIFIN SHIGAR MATA
Yan sanda a kasar Uganda sun kame wani mutum da laifin yin kwalliya a matsayin mace da kuma satar mazan da ba su ji ba basu gani ba. 
Mutumin,(an sakaya suna wanda ke sanye da kayan mata, an kama shi ne a cikin makon nan bayan wani wanda ba a san ko wanene ba ya kai rahotonsa da yin kwaikwayo da shiga irin ta Mata zuwa ga ofishin ‘yan sanda kamar yadda Alkibla ta rawaito. Domin tabbatar da jinsinsa, ‘yan sandan sun umarce shi da ya cire kayan dake jikin sa. 
Ya zuwa yanzu, mutane 57 sun tabbatar da cewa wanda ake zargin ya damfare su ya yin da mutane 22 wadanda abun ya shafa suka ce ya damfare su fiye da sau uku.

Post a Comment

Previous Post Next Post