YADDA ADAMU ALERU DA SAURAN 'YAN BINDIGAR DAJI KE SAYEN DABBOBI A YANZU
Rahotannin da ke shigowa ASKGLOCNEWS na cewa, a yanzu 'yan bindigar daji sun mayar da hankali ga sayen shanu, tumaki da awaki maimakon zuwa satowa ta amfani da ƙarfin bindigar da aka san su da yi a baya. Wata majiya mai tushe (an sakaya suna) daga garin Ɗanjibga dake Jahar Zamfara ta shaida mana cewa a yanzu a duk ranar kasuwar garin wadda ke ci a ranar alhamis sai anga ɓarayin shanun da yin garkuwa da mutane sun shigo kasuwar don sayen dabbobin maimakon nuna ƙarfin bimdiga su kora kamar yadda suke yi a baya.
Majiyar tace wannan sabuwar dubarar da ɓarayin shanun ke yi bata rasa nasaba da batun canjin kuɗin da Babban Bankin Najeriya ya bayar da sanarwar yi, wanda hakan ya tilasta masu mugayen kudaden da suka tara ta hanyar karbar kudin fansar da suka riƙa yi a baya. "Gudun kada su yi asara yasa yanzu suke fiddo kudin suna sayen shanu da duk wani abin da suke bukata ba kuma tare da yin la'akari da tsadar abin sayarwa ba, suna yin haka ne don gudun yin asarar abin da suka tara".
Daga cikin manyan ɓarayin shanun dake zuwa wannan kasuwa don sayen shanu har da shaharren ɗan bindigar nan wanda har zuwa rubuta wannan labari rundunar 'Yansanda da gwamnatin Jahar Katsina ke neman shi ruwa a jallo har ma da ladar kuɗi ga duk wanda ya kawo shi ko yayi sanadiyar kawo, wato, Adamu Aleru Ɗandoto. Shi ne wanda akwanakin baya wata masarauta a Jahar ta Zambara ta bashi sarauta, abinda gwamnatin Zamfarar ta nisanta kanta har ma ta tuɓe sarkin da ya bayar da wannan sarauta ta Sarkin Fulanin 'Yandoton daji da aka yi mashi.
Majiyar tace, ko a wannan satin, Adamu Aleru ya shigo kasuwar kuma ya sayi shanu fiye da yadda ake zato. "Wato, in kunga yadda ake kashe kudi a wurin abin akwai ban tsoro, saaboda babu ruwan su da tsada, suna wasa da nera fiye da tunani. Waɗannan 'yanbindiga suna yawon su hankali kwance, ba ma kamar shi Aleru duk kuwa da cewa, ga jami'an tsaro. Shin an janye wancan batun na kama shi ko kuwa ita hukumar 'yansandan ba guda bace a ƙasar? Wato ko wane sashe babu ruwan shi da sashen da baya ƙarƙashin shi?
Yanzu dai abin da ake sauraren gani ko ji shi ne, shin ina waɗannnan barayin dajin zasu kai shanun da suke saye, sannan ina waɗanda suka kwace daga jama'a? Kazalika, idan har lokacin da aka bayar na batun canjin kudin yayi basu ɓatar da nasu ba, yaya za'a yi. Shin wannan yana nuni da kawo ƙarshen neman kuɗin fansa ko kuwa akwai wani abin da zai biyo baya?