ƘUNGIYAR ZABI SON KA TA JAHAR KATSINA NA NEMAN OFIS

ƘUNGIYAR ZABI SON KA TA JAHAR KATSINA NA NEMAN OFIS

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 

A wani ƙwarya-ƙwaryan taro da ƙungiyar zabi son ka da taimakon juna reshen Jahar Katsina ta gudanar a harabar gidan rediyon jahar a ranar asubucin wannan sati 12 ga watan Nuwamba 2022 ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar Alhaji Ya'u Emiya. Ƙungiyar tayi kira ga masu hali da su tallafa mata da ofis ko kuma filin da zata gina ofis acikin Jahar. 
Shugaban ƙungiyar na jaha yayi wannan roko ga jama'ar jahar wanda yace, ƙungiyar jahar ce kaɗai ke koma baya ga mallakar ofis a duk fadin ƙasar. "Mun zagaya wurare da dama acikin ƙasar nan kuma mun ga irin yadda ƙungiyoyin suka mallaki ofis wanda mafi yawan su sunce tallafi ne daga jama'a duba da irin tasiri da kuma tallafin da ƙungiyar ke bayarwa ta fannin taimakon kai da kai, gyaran maƙabartu da sauran irin su. Sannan ga hada zumunci da suke yi wanda ya ƙara da cewa, a wasu lokuttan ma har tallata hajar mutun da suke yi a lokacin da ake rubutawa tare da karanta katin zabe a tsawon shekaru da suka wuce. "Misali, shugaba Inunu mai Dankalin turawa, Malam malan mai zanen hula, Hajiya Asibi mai abinci da sauran irin su".
Da aka juya wajen batun katin sheda na membobin ƙungiyar da har yanzu wasu basu da shi, shugaban ya bayar da umarni nan take da kowace ƙaramar hukuma taje ta cigaba da sayarwa membobin ta da wannan katin sheda.
Alhaji Ya'u bayan jinjinawa ya ƙara yin godiya ga hukumar gidan rediyon wanda yace, kullum suna samun goyon baya, kuma duk wani taro in sun tashi yi, anan suke zuwa suyi ba'a taɓa nuna masu damuwa ba duk da kasancewa ma'aikata ce ta gwamnati. 
Shugaban ya ƙara yin kira ga 'ya'yan ƙungiyar da su cigaba da basu hadin kai kamar yadda aka saba. 

Post a Comment

Previous Post Next Post