RASHIN MUTUNTA MU YASA MUKA BAR APC - Anas Rabe
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Matashin ɗan siyasa kuma ɗaya daga cikin matasan da jam'iyar APC a Jahar Katsina take alfahari da su yace, sun bar jam'iyar ne suka koma ta PDP sakamakon rashin mutuntasu da yace aka rika yi tun bayan yin zaɓen fidda gwani na jam'iyar da aka yi. Anas Rabe Kafinta wanda yake tare da tsohon Sakataren gwamnatin Jahar Dokta Mustafa Inwa wanda bai samu nasarar cin wancan zaɓe ne na fidda gwani yace, "tun bayan yin wancan zaɓe har zuwa ranar da muka fita daga jam'iyar babu wani ko wasu a jam'iyyance da suka sake tuntubar shi Maigidanmu duk kuwa da irin rawar da ya takawa jam'iyar a zaɓen 2015 da 2019. Hasali ma sai aka fara yi mana wasu maganganu na barazana cewar za'a kore mu daga jam'iyar.
Ganin haka, yasa shi Dokta duk da cewa, sauran jam'iyu sun ta kawo mashi ziyarar neman goyon bayan shi ya kuma shiga cikin su, wadda har jam'iyar "Labour" lokacin da shugaban ta na ƙasa ya zo wajen shi, yace, zasu bashi takarar kujerar Gwamna. Amma Dokta yace, shi ba ta jam'iya ko takara ke gaban shi, a'a, ci gaban al'ummar jahar ne yasa gaba. Hatta da shugaban jam'iyar NNPP na ƙasa Dokta Kwankwaso ya turo wakillan shi, amma Dokta baice masu komai ba. Kawai amsar da yake bayarwa ita ce, inda jama'a suke so shi can za shi. Mu kuma mune muka sanya shi komawa jam'iyar PDP. Anyi haka ne duba da irin ƙarfin jsm'iya wadda ake ganin zata ci zaɓe. To kuwa anan jahar Katsina PDP ce muke sa ran da ikon Allah zata ci zaɓen 2023 in Allah ya kaimu.
Da yake amsa tambayar ko dame zasu yiwa jama'a ganin cewa da su aka yi APC? Anas Rabe yace, ai ba sai sunce komi ba, jama'a alkalai ne akan abinda yake faruwa. Duk wasu surutai da aka yi a baya, ai yanzu ga shi 'yarfage ta nuna. Sannan wani abin farin ciki anan shi ne, duk da ba wani dogon lokaci muka ɗauka ba a shigowar mu a PDP amma saboda jam' iya ce mai tsari wadda ta san mutuncin mutane, yau ga shi Dokta Mustafa shi aka ba Daraktan yaƙin neman zaɓen Atiku da Lado. Ni nan kaina ina cikin membobin kwamitin yaƙin neman zaɓen da aka zaɓo mutane sama da ɗari bakwai da za'ayi tafiyar da su, saɓanin inda acan muke", inji matashin ɗan siyasar Anas Rabe Kafinta.