MAI UNGUWAR DAKE BA 'YAN BINDIGAR DAJI JAMA'AR SHI SUNA KASHEWA YA SHIGA HANNU A KATSINA

MAI UNGUWAR DAKE BA 'YAN BINDIGAR DAJI JAMA'AR SHI SUNA KASHEWA YA SHIGA HANNU A KATSINA 
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
Dubun wani Mai Unguwar dake baiwa 'yan bindigar daji al' ummarsa suna kashewa. Mai Unguwa Surajo Madawaki na garin Gobirawa dake cikin Æ™aramar hukumar Faskari shi ne wanda ya faÉ—a komar jami'an 'yan sanda bayan ya ari takalman kare ya É“oye bayan da asirin shi ya tonu akan miÆ™awa 'yan bindigar daji wani talakkan shi mai suna Yahaya Danbai inda suka kashe shi. 
Kamar yadda jami'in hudda da jama'a na rundunar 'yansandan Jahar Katsina Sufurtanda Gambo Isa ya gabatarwa manema labarai Mai Unguwar da ake zargi a ranar 18 ga watan Nuwamba na 2022, Sufurtandan yace, ana zargin Mai unguwar akan miƙa wannan matashi wanda Allah ya ba nasarar kashe wani ɗan bindiga da yayi yunƙurin yin garkuwa da shi a lokacin da shi wannan matashi mai suna Yahaya yake cikin aikin gonarsa. Yahaya ya samu yin galaba akan wannan ɗan bindiga inda Allah ya bashi sa'ar kashe shi. Yahayan ya ɗauko bindigar wannan ɗan ta'adda mai ƙirar AK47 ya kuma kawowa Mai unguwa ita tare da yi mashi bayanin abin da ya faru, amma maimakon shi Mai unguwa Surajo ya nemi hukuma don miƙa wannan bindiga kamar yadda aka yi mashi, sai ya kira ɗaya daga cikin shugabannin 'yan bindigar dajin mai suna Hamisu ya miƙa mashi wannan bindiga domin ta yaron shi Hamisun ce.
Ganin haka, yasa shi Hamisu da sauran tawagar shi suka azawa mutanen garin biyan naira milyan goma ta diyyar yaron su da aka kashe, sannan suka tafi da shi Yahaya suka kashe. Sun sha alwashin in ba'a basu waÉ—annan kudade ba, zasu kashe duka mutanen garin.
A nashi jawabin Mai unguwa Yahaya yace, lallai bai ba Magaji ko Hakimi ko jami'an tsaron dake wannan yanki bindigar ba saboda gudun abin da ka iya biyowa baya daga su wajen 'yanbindigar ba wanda yace sune masu faÉ—i aji a yanki. Saidai ya musanta cewa, shi ya kira su Hamisu bai kuma san yadda aka yi suka samu labarin ba. Amma ya danganta jin labarin nasu abu ne mai sauki tunda a bainar jama'ar gari aka taho da ita, kuma akwai  'yanbindigar nan acikin garin waÉ—anda basu iya yi masu komai. Har ila yau, ya tabbatar da tafiya da shi Yahaya kuma sun kashe shi. 

Post a Comment

Previous Post Next Post