GWAMNA MASARI YA BUƊE CIBIYAR NOMAN SHINKAFA A KATSINA

GWAMNA MASARI YA BUDE CIBIYAR NOMAN SHINKAFA A KATSINA 
Daga Ya'u Bersho, Katsina 

"Duk kasashen duniya da kuka ji sun ci gaba, hakika noma suka rike". Kalamin da ya fito daga bakin Gwamnan Jahar Katsina Alh Aminu Bello Masari a lokacin da yake bude cibiyar koyan noman shinkafa a garin Raɗɗawa dake karamar Hukumar Matazu, da kuma Maƙera dake ƙaramar hukumar Dutsinma, aikin na  hadin gwiwa ne tsakanin "Saemaul Foundation" daga ƙasar Korea ta Kudu tare da gwamnatin Jahar ta Katsina, bikin budewar da aka yi a ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba, 2022. 
           
 Gwamna Masari ya ce, kamar yadda Daraktan Ƙasa Kyungbok Lee ya fadi cewa Kasar su ta Korea ta Kudu, shekaru sittin da suka wuce suna cikin talauci, amma tunda suka kama noma sai arziki ya yadu a kasar gashi yanzu suna cikin jerin kasashen duniya masu arziki. Saboda haka yana da kyau muma anan mu rungumi noma domin arziki yana tare da noma tunda Allah Ya bamu ruwa, Ya bamu kasar wannan shine babban arzikin da Allah Ya bamu sai dai idan bamu so ne kawai. Gwamna Masari ya cigaba da cewa, "zaman lafiyar mu shine mu rike noma ku kuma wadanda aka koyama wannan noma na shinkafa to kuje ku koyama makwabtan ku da 'ya'yan ku sai ku zauna lafiya". Gwamnan ya ƙara da cewa, "ku sani duk abinda zaka ci ko ka sha to daga noman nan yake, dan haka ya zama dole mu yabama Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da yace a koma gona, yanzu gashi noman ne yake rike da Kasar.
" Wannan shiri ba maganar siyasa bace magana ce ta ciyar da al'ummar Jihar Katsina gaba, saboda haka kowa yayi kokari ya koyi wannan noma musamman ma ku matasa". 
Har'ila yau, Gwamna Masari yayi kira ga 'Yanɗakan Katsina hakimin Dutsinma da ya zama mai sa ido a cibiyar koda bayan sun sabka daga mulkin, domin cigaban yankin ne. 

Mairgirma Gwamna yayi godiya ta musanman ga Country Director Kyungbok Lee Shugaban Samemaul Foundation da sauran yan tawagar sa da su ka zo Nigeria kuma Jihar Katsina domin su koyama mutanen Jihar Katsina noman shinkafa na zamani wanda ko shakka babu ba karamin cigaba bane a Jihar.

A nashi jawabin, Mista. Kyungbok, shugaban "Saemaul Foundation", wato, Gidauniyar Saemaul, yace suna godiya ga Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Alh Aminu Bello Masari da sauran muƙarraban gwamnati da masu ruwa da tsaki a wannan sashe bisa wannan dama da Gwamnatin Jihar Katsina ta basu domin yin hadin gwiwa dasu don habbaka noma a Jihar Katsina. Ya ƙara da cewa, dama shekarun baya suna da kyakyawar alaka tsakanin kasar su ta Korea ta Kudu da Nijeria, kuma yanzu gashi alakar ta sake kulluwa. Yace sun zabi su koya ma yan Jihar Katsina noman shinkafar ne domin su zamo masu dogaro da kan su kuma arzikin Jihar ya habbaka. Ya cigaba da cewa daga cikin ayyukan da Gidauniyar tasu zasu yi sun hada da koyon noman rani na shinkafa, samar da hanyoyi na karkara wato rural roads, gyaran makarantun boko da daga darajar asibitoci na karkara wanda tsawon shekarun aikin zai kai shekara biyar, haka kuma aikin zai ci dala miliyan biyar ($5m).

Post a Comment

Previous Post Next Post