FAMWAN TA BUKACI 'YA'YAN TA SU YI RIJISTSR A ZAƁE A JAHAR JIGAWA

FAMWAN TA BUKACI 'YA' SUYI RIJISTAR ZAƁE A JAHAR JIGAWA
Umar Akilu Majeri, Dutse
An bukaci 'ya'yan Ƙungiyar Musulmi Mata ta FAMWAN a duk inda suke a Jahar Jigawa da su yanki katin zabe domin kare mutuncinsu da na addininsu domin wani lokaci zaizo nan gaba da gwamnati zata ce wasu abubuwan more rayuwa baza a anfana dasu ba sai anada katin zaɓe da katin ɗan ƙasa. 
Shugabar ƙungiyar Hajiya Maimuna Ahmed Abubakar ce tayi wannan kiran a wata ganawa da wakilinmu na Jahar Jigawa a Birnin Dutse. Ta kuma bukaci gwamnati da masu hannu da shuni su agazawa kungiyar wajan gyara makarantarsu da islamiyya da suke koyarwa matan aure da 'yan mata da zawarawa bayan samun matsala da makarantar tayi a lokacin damina wadda take bukatar gyare gyare .
Da take bada tarihin kafuwar ƙungiyar ta FAMWAN shugabar tace an kafa ta domin yaɗa manufar addinin musulunci tun kimanin shekaru talatin da suka gabata. Tace kara da cewa, 'ya' yan ƙungiyar sun fuskanci kalubale masu yawa kasancewar wadda ta kawo kungiyar a Najeriya wata baturoyace matar wani alkali a Najeriya da ake cewa Lemu. Sai wasu suka riƙa yiwa ƙungiyar mummunar fasara da cewar wata ƙungiyace da zata farraƙa kan matan aure. 
Hajiya Maimuna tace yanzu ƙungiyar sai san barka domin al,amuranta sun tafo daidai saboda al,umma da dama sun fahinci manufarta. Yanzu haka qungiyar FAMWAN ta shiga sako da loko a ɗaukacin ƙananan hukumomin Jahar Jigawa 27 tana yaɗa manufarta 
Wani abin alfahari inji Hajiya Maimuna Abubakar aƙarƙashin jagorancinta sun musuluntar da maguzawa sama da 29 ayankin ƙaramar hukumar Roni dake Jahar. 
"Sakamakon amsar kalma shahada da waɗancan maguzawa sukayi yanzu haka mafiya yawan al'ummar wancan kauye dake cikin qaramar hukumar ta Roni sun shiga musulunci" 
Da ta juya wajen yadda sukewa addini hidima tace  sun gina masallatai a kauyuka a yankin Roni da qaramar hukumar Kiyawa da nufin habaka addinin Allah. 
Sai dai Hajiyar ta koka akan ƙarancin kudi da suke fuskanta wadanda da sune suke fita wa,azi da gudanar da aiyukan yau da kullum. Saboda haka ta roki al'ummar Musulmi a duk inda suke da su shigo su bada tasu gudunmawar wajen gina addinin Allah.
Akan batun siyasa shugabar cewa tayi ƙungiyar su bata da alaka da siyasa domin siyasa ra'ayice kowa yana da na shi. Amma dai 'ya'yan ƙungiyar su natsu wajen anfani da kwakwalwarsu su zabi mutane nagari masu kishin addini wadanda zasu taimakawa addinin musulunci. 

Post a Comment

Previous Post Next Post