DUKKAN ALAMU SUN NUNA APC ZATA CINYE ZABEN 2023 - Sanata Abu Ibrahim
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Tsohon ɗan majalisar dattawa kuma jigo a jam'iyar APC yace, dukkan alamu sun nuna cewa, jam'iyar APC ce zata yi nasara a dukkan zabubbukan da za'a yi a 2023, inda yace, ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa Ahmed Tinubu da kuma a jahar shi ta Katsina.
Sanata Abu Ibrahim ya baiyana haka ne a wani taron mamema labarai da yayi a ranar talatar nan a Katsina bayan kammala wani taron sasanci da ya jagoranta a garin Musawa tare da 'ya'yan jam' iyar da suka fito daga shiryar shi ta Funtuwa. Taron sasanci an shirya yin shi ne domin baiwa waÉ—anda aka yiwa ba daidai ba hakuri, kazalika, tare da kawo jituwa ga wadanda ke da wannan matsala, tare kuma da neman afuwa ga waÉ—anda aka sabawa.
"Na jagoranci wannan taro ne domin ganin irin yadda jama'a ke girmamani kasancewa ta wanda yayi shekaru sama da goma yana Sanata daga shiyyar Funtuwa a Jahar Katsina. Ganin wasu in aka ce ana neman su ba zasu zo ba in suka ji masu shirya taron yasa naga cewa, to bari in jagorance shi. Kuma Allah cikin ikon shi ya bamu nasarar samun fahimtar juna kuma aka sasanta bayan yafiya. Abin ma da ya ƙara burge ni ya kuma bani ƙwarin gwiwar cewa, lallai jam'iyar mu zata yi nasara da kaso mafi tsoka a zaben 2023 musamman jahar Katsina, shi ne ta yadda wani daga cikin waɗanda aka samu rashin jituwa a baya, yau sai ga shi ya bayar da motocin shi domin cigaba da hidimomin jam'iya wanda hakan ya nuna a fili, har yanzu muna nan a matsayin tsinstiyarmu mai madauri guda".
Sanata Abu Ibrahim ya ƙara da cewa, hakika an samu kurakurai a lokacin mulkin jam'iyar APC na shekaru 7 da tayi musamman akan abin da jama'a ke koke na batun rashin tsaro. "Maganar rashin tsaro babu wanda zaice ba'a fuskantar haka, amma ba kamar a baya ba inda saida aka samu wasu ƙananan hukumomi sama da 10 suke hannun 'yan Boko Haram. Sun mamaye komi aciki, amma yau babu sauran koda ƙaramar hukuma guda dake hannun su. Sannan waɗannan.'yan bindigar dajin na yanzu, duk da cewa, su ma akwai masu ɗaure masu gindi, su ma da ikon Allah an kusa gamawa da baki daya".
Daga ƙarshe Sanatan bayan ƙara jaddada cewa babban kwamitin da jam'iyar ta kafa a Jahar wanda shine zai tsara komai dangane da batun zabubbukan da za'a yi, yayi kira ga jama'a da su ƙara ba jam'iyar goyon baya ta hanyar zaben dukkan 'yan takarkarun da ta tsaida.