Da dumi dumi MAX AIR ZASU FARA JIGILA DAGA LAGOS ZUWA KATSINA

Da dumi dumi MAX AIR ZASU FARA JIGILA DAGA LAGOS ZUWA KATSINA 
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
Kamfanin jiragen Max Air mallakar shaharren ɗan kasuwar nan dake Katsina Alhaji Dahiru Mangal zasu fara zirga-zirgar ɗaukar fasinjoji daga Lagos zuwa Katsina domin ƙara sauƙaƙawa matafiya. 
Kamar yadda ɗaya daga cikin majiɓanan wannan kamfani Alhaji Dikko Dahiru Mangal ya sanar, za'a fara jigila ta musamman a tsakanin Lagos zuwa Katsina a ranar Talatar nan 15 ga watan Nuwamba, 2022 da misalin ƙarfe 7 na safe zuwa filin jirgi na Umaru Musa dake Katsina. Kazalika, jirgin Max Air zai tashi daga filin jirgin daga ƙarfe 5 na yamma domin zuwa Lagos a wannan rana. 
Tuni dai wannan kamfani yake Zirga-zirga a tsakanin Katsina da Abuja a ranakun Litinin da Laraba da kuma juma'a a kowane sati. Kamfanin Max Air dai ya zamo kamfani mafi shahara a wajen ɗaukar maniyatan aikin hajji aciki da wajen Nigeria. 

Post a Comment

Previous Post Next Post