Bichi - APC TA ƘADDAMAR DA KWAMITIN YAƘIN ZAƁEN 2023 DA ZUMMAR SAMUN NASARA - Dokta Sabo.
Daga Jabiru Hassan
Shugaban Karamar hukumar Bichi Dokta Yusuf Mohammed Sabo yace kwamitin yakin neman Zabe da jam'iyyar APC ta kafa a karamar hukumar zai yi aiki sosai domin ganin jam'iyyar ta nasara ta hanyar lashe zabukan shekara ta 2023 da za'a yi tun daga sama har kasa.
Shugaban kwamitin yaƙin zaben
Injiniya Abubakar Kabir Abubakar
Da yake gabatar da jadawalin mambobin kwamitin ga masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ta APC Dokta Yusuf Mohammed Sabo, yace ko shakka babu, dukanin mambobin wannan kwamiti mutane ne jajirtattu wajen hidimar jam'iyyar ta APC wanda hakan ke nunar da cewa kwalliya zata biya kudin sabulu.
Yace dukkanin wadanda sunayen su ya fito a jadawalin mambobin kwamitin mutane ne masu kokari kan harkokin jam'iyyar APC tun lokacin da aka kafa ta, kuma an ga irin gudummawar da suke bayarwa batare da nuna kasala ba.
Yayi godiya ta musamman ga shugaban kwamitin kuma Dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bichi, Injiniya Abubakar Kabir Abubakar saboda gagarumar gudummawar da yake bayarwa wajen bunkasa jam'iyyar ta APC da kuma samar da ribar dimokuradiyya a fadin karamar hukumar.
Dokta Sabo ya mika godiyar sa ga daukacin al'umar karamar hukumar Bichi saboda goyon baya da hadin kai da suke baiwa gwamnatin sa da kuma jam'iyyar APC tareda yin alwashin cewa akwai tanade-tanade masu albarka da jam'iyyar take dasu domin kara inganta rayuwar su.
A karshe, ya yabawa gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda kokarin da yake yi dare da rana wajen ganin jam'iyyar APC ta same nasara a zaben 2023 a jihar Kano da kuma kasa baki daya, tareda bayyana cewa suma a matakin kananan hukumomi, zasu ci gaba da bin sahun gwamnan wajen samar da nasarar jam'iyyar a kananan hukumomin su.