ANA TUHUMAR ƊAN SHEKARA 75 DA YIWA JIKAR SHI MAI SHEKARU 6 FYADE

ANA TUHUMAR ƊAN SHEKARA 75 DA YIWA JIKAR SHI MAI SHEKARA 6 FYADE - NSCDC 

Daga Umar Akilu Majeri a Dutse

Rundunar tsaro ta farin Kaya da Kare dukiyar jama,a NSCDC ta kasa reshen jahar JIgawa dake aiki  a karamar hukumar Malammadori ta Sami  nasarar chafke wani tsoho mai kimanin shekaru Saba'in da biyar a duniya bisa zargin yiwa wata yarinya Yar shekara shidda fyade. 

Tsohon da akace  yana zaune a unguwar Gandun sarki dake cikin garin  Hadejia mai suna Gambo Musa an kama shi kuma yana tsare a hannun Hukumar tun ranar Sha shida ga wannan watan na Nuwamba 2022. 

Ya faɗa hannun hukumar ne a lokacin da wata Mata ta kama shi turmi da taɓarya kuma ta sanarwa uwar yarinyar Hajiya Maimuna ita Kuma uwar yarinyar wadda 'yarsace, ita ce ma tabashi dakin da yake zaune agidanta kasancewar ya Jima ba shi da mata. 

Faruwar haka yasa matar ta garzaya ofishin Jami an tsaro na unguwar Gandun ta shaidawa Jami' an tsaro inda suka damkeshi ba tare da ɓata lokaci ba. 

 Kamar yadda bincike ya nuna tsohon ya jima rabonsa da gida sai kwanaki ya dawo, ya kumam dawo ba tare da mata ba, hakan yasa yake zaune gida guda da wannan 'yar uwa tashi wadda take mahaifiyar uwar wannan yarinya ce, wato, jikar shi kenan. 

Yarinyar tace kakan nata yagargaɗe ta da kada ta faɗawa kowa, in kuma ta kuskura ta faɗi shi kaɗai yasan abin da zaiyi mata, to sai Allah ya toni asirin shi aka kama su.

Yanzu haka dai  za'a gurfanar da tsohon agaban kotun shari'ar musulunci domin ya fuskanci hukuncin akan laifin da ya aikata 

Tuni dai rahoton binciken likitoci ya tabbatar da an taɓa matuncin yarinyar wanda hakan yasa Gambo amsa cewar lallai ya aikata laifin da ake zargin shi da aikatawa. Ya kuma roki da ayi mashi sassauci a bisa wannan kuskure wanda yace kaddara ce ta sa ya aikata. 

Post a Comment

Previous Post Next Post