ABUBUWA UKKU KE HANA HADIN KAI... SAI BANGARORI BIYU SUN HADU AKE SAMUN HADIN KAI - Malamai

ABUBUWA UKKU KE HANA HAÆŠIN KAI....
...SAI BANGARORI BIYU SUN HADU AKE SAMUN HADIN KAI - Malamai
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
A ranar lahadi 27 ga watan Nuwamba 2022 aka gudanar da karatun Al Kur'ani mai girma tare da yin addu'o'in musamman domin Æ™ara samun zaman lafiya tare da neman Allah ya kawo Æ™arshen matsalar tsaron da ake fama da shi a Jahar Katsina da Æ™asa baki É—aya tare kuma da Æ™ara neman haÉ—in kai a tsakanin al'umma. 
          
Ofishin Mai baiwa Gwamna Masari shawara akan sha'anin tsaro ƙarƙashin jagorancin Alhaji Ibrahim Muhammad Katsina ya shirya domin ganin Jahar ta koma turbarta ta asali wadda aka sani da zaman lafiya da haɗin kai. Taron anyi shi a masallacin Jumma'a na Bin Fodiya dake kusa da gidan gwamnatin Jahar a garin Modoji, wanda ya samu halarcin malamai da ɗaliban ilmin da suka fito daga ɓagarorin Izala da Ɗarika tare da 'yan Ƙur'aniyu,dukkan su sun haɗu wajen karatun ƙur'ani da addu'o'in.
A saƙon da ya aika a wajen wannan taron karatun Ƙur'ani da addu'o'in, Mai Martaba Sarkin Katsina Dokta Abdulmuminu Kabir wanda Alkalin Lardi, Ahmad Ibrahim Batagarawa ya wakilta, Sarkin ya nuna damuwar sa akan rashin haɗin kai da ake samu a tsakanin musulmi. Sarkin ya kawo misali da irin yadda banbancen akida da kuma rashin jituwar da ke akwai a tsakanin mabiya addinin kirista, amma hakan bai hana su hada kai wuri guda idan maganar addini ta shigo suna hade kansu wuri guda su manta da waccan gabar dake tsakani su amma banda musulmi. Sarkin ya ja hankalin jama'ar musulmi akan muhimmancin haɗin kai acikin dogon bayanin da yayi.
Shi kuwa shugaban ƙungiyar malamai na Jahar Sheik Nazir Kofar Baru Daura, ya ja hankali ne akan irin yadda ake mulakanta mutun bayan Allah ya faɗi cewar ya karrama ɗan-Adam. Malamin ya baiyana irin yadda ake ciwa ɗan Adam mutunci a yanzu musamman daga sashen masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa. Irin yadda ake tozarta mutane da cin zarafin mata da yara ƙanana da sauran su, wanda yace ko yin hakan na iya jefa mu cikin fitinu iri-iri. Malamin daga nan sai yayi faɗakarwa akan son juna da kuma kiyaye dokokin Allah da yin biyayya gare su kamar yadda suka zo acikin Al-Ƙur'ani.
A tashi nasihar, Sheik Sukaraju Dutsinma baiyana wasu dalilai yayi dake hana samun haɗin kai acikin al'ummar musulmai. Na farko kamar yadda malamin yace, Riya. Ya baiyana a fili cewar, Riya na daga cikin abubuwan dake hana hadin kai,domin ana yin abu ba don Allah ba, shi kuma Allah sai ya lalata abin. Sai na biyu ita ce Hassada. A cewar malamin duk mutumin da zai yiwa ɗan-uwan shi hassada, to Allah bai karbar aikin shi balle wani abu hadin kai ya shigo. Sai na uku wadda ita ce Giba. Wato, masu yi da 'yan-uwansu bayan idon su. Ya kawo wani misali a lokacin rayuwar Annabin tsira inda yace, "wata ana zaune a fadar Annabi, sai sahabbai suka riƙa jin wani wari yana fitowa har suka kai suna tambayar ko warin menene, sai Annabi yace masu, warin bakunan masu yi da 'yan-uwan su ne ke fitowa". Sheik Sukarajo ya ja hankali akan cewa, muddin ana son haɗin kai a tsakanin al'umma, to lallai sai an kiyaye waɗancan abubuwa uku.
Shi kuma Imam Samu Adamu, cewa yayi, raba kawunan mutane biyu ne yasa sauran jama'a suka rabu. "Raba kan shugabanni da malamai, inda aka nuna kowa ya ci gashin kan shi, to anan ne matsalar rabuwar kawuna ta samu. Ai a lokacin Annabi, shi ne komi, wato, shugaba kuma malami. Haka sahabban shi suka yi. Sannan yana da kyau jama'a su gane wani abu guda, wato, gabar dake tsakanin kiristoci da Yahudawa. Domin kirista yayi imani bayahude ya kashe mashi Annabi(mu kuma mun san ba haka bane). Amma da zarar ance, za'a yaƙi musulunci dukkansu sun haɗu don a samu nasara. Kai yau an wayi gari hatta da 'yanluwadi, ɓarayi,'yan ƙwallo da sauran su duk suna hada kai amma banda musulmi saboda kawai bambamcin ra'ayi ko aƙida. Amma kuma fa an haɗu a Ƙur'ani guda, al Ƙiblar salla guda, hatta da Ɗawafin aikin hajji duk iri ɗaya ake yi, amma kuma haɗin kan yake yin wuya kawai saboda kada a samu ƙarancin magoya baya, maimakon a haɗu a tunkari wata matsala ko wani abu in ya taso don ayi nasara. Su ma ɓangaren shugabannin haka abin yake, musamman da siyasa ta shigo".
Kazalika,shi ma Maigirma Gwamnan Jahar Alhaji Aminu Bello Masari acikin tambayoyin manema labarai yace, addu'a ita ce babban makamin mumini, kuma ita babban abin da ke kawo ƙarshen kowace irin matsala. Bisa wannan dalili ne yasa gwamnatin shi ta ƙara bayar da himma a wajen yin addu'o'in godiya ga Allah da kuma neman taimakon shi don yayewa jahar duk wata fitina. "Anan Jahar Katsina mutane waɗanda muka yarda da Allah kuma muka yarda da cewa yin addu'o'in suna taimakawa wajen yin domin Allah ya kawo mana saukin abubuwan da ake yi. Ai mutun ko tafiya zaiyi zuwa wani wuri, cewa yake yi Allah ya kaimu lafiya. Akan haka yasa mu duk abubuwan da muke yi muna yi masu shimfida ne da addu'a,domin Allah yasa kwalliya ta biya kudin sabulu.
Kazalika, wanda ya shirya wancan taron addu'o'in kuma Mai baiwa Gwamna Masari shawara akan sha'anin tsaro Alhaji Ibrahim Muhammad Katsina yace, batun yin irin waÉ—annan addu'o'i ba abu ba ne wanda za'a ce daga lokaci zuwa lokaci za'a yi su ba. Ita addu'a kullum yin ta ake yi kuma tana Æ™ara haÉ—a kan al' umma da kawo zaman lafiya. Ya Æ™ara da cewa, hatta da matsalar tsaro da ake fama da ita a Jahar, yanzu sai dai a cigaba da yiwa Allah godiya saboda an samu sauÆ™in matsalar da kusan kashi 85 zuwa 90 cikin É—ari in aka tuna yadda abin yayi ta faruwa a can baya. 

Post a Comment

Previous Post Next Post