2022 Hajj MANIYATA 101 SUKA KARBI KUDIN SU A KATSINA

2022 Hajj MANIYATA 101 SUKA KARBI KUDIN SU A KATSINA

Daga Kabir Ahmed S/Kuka

Hukumar jin daÉ—in alhazai ta Jahar Katsina ta fara mayarwa maniyatan da basu samu damar zuwa aikin Hajjin 2022 ba. 

   Kamar yadda wata sanarwar ta fito daga jami'in hulda da jama'a na hukumar Alhaji Badaru Karofi ta ce, an fara bayar da cekin kudi ga jami'an shiyya na hukumar wanda Daraktan kudi na hukumar Alhaji Sagir Abdullahi Inde kuma Sarkin Musawan Katsina ya bayar da cekin kudin a madadin Babban Daraktan hukumar Alhaji Sulemain Nuhu Kuki a hedkwatar hukumar dake cikin garin a ranar Litinin 7 ga watan Nuwamban 2022.
Hukumar ta mayar da naira milyan É—ari da talatin da uku da dubu É—ari biyu da tamanin(N133.280.000.00) ga maniyata É—ari da É—aya(101)da suka nemi a mayar masu da kudaden su. Daraktan kudin yace, wannan kashin farko da hukumar ta fara biyan ga duk mai son a mayar mashi da kudin shi, kamar yadda yake acikin tsarin aiyukan hukumar. Sai dai yace, masu son barin na su kudaden a matsayin ajiya don shirin aikin Hajjin mai zuwa, su ma suna da damar yin haka ga hukumar.
  Indai za'a iya tunawa, Jahar Katsina ta samu yawan kujeru 2.446 daga hukumar alhazai ta Æ™asa kasancewar ba'a samu sanarwar yawan kujeru daga Æ™asar ta Saudiya sai a kuraren lokaci, kuma babu kujeru masu yawa da aka samu. Ƙarancin kujerun da kuma matsalar biza da aka samu, hakan yasa wasu maniyatan basu samu damar zuwa aikin ba. Hasalima, hatta daga cikin maniyatan da aka ba Jahar ta Katsina, maniyata 2,069 ne suka samu zuwa gami da jami'an hukumar 12 waÉ—anda jimlar su suka kama 2,081.
   Kamar yadda Babban Daraktan hukumar ya taÉ“a cewa a wata hira da aka yi shi, tabbas a aikin Hajji na 2022 ba zasu karbi kudin kowa ba sai sun tabbatar da cewa, waÉ—anda suka biya kudin su tun daga bayan dawowar aikin Hajjin 2019 domin samun tafiya a na 2020 wanda tafiyar bata samu ba suka yi hakuri duk da cewa wasu sun amshi nasu kudin, amma har aka samu wadanda suka ajiye a don tafiya 2021 suma saboda lalurar da aka samu ta cutar korona. Alhaji Sulemain yace, duk lokacin da aka samu damar tafiya, to waÉ—anda suka bar kudaden su sune na farko, haka kuma abin ya faru.
Kamar yadda muka samu bayanai, sunce hukumar ta bi tsari na yadda ta riƙa dauko maniyatan daki-daki, wato, wanda ya riga shi za'a fara da shi. In baya ga matsalar bizar da aka samu, hakika ta shirya kwashe duk maniyatan da kudin su suka dade a hannun hukumar.
  Yanzu haka dai hukumar na cigaba da shirye-shiryen daukar masu son zuwa aikin Umra a hukumance, wanda kuma shi ne karon farko a tarihin hukumar ta Jahar Katsina. 

Post a Comment

Previous Post Next Post