Zaben 2023 AN YI TARON MASU RUWA DA TSAKI A SHIYYAR FUNTUWA
Daga Sa'adu Saulawa
Kasancewa an bude fagen yakin neman zabe domin gudanar da zabubbukan shekara ta 2023 Jami an tsaro a shiyyar Funtuwa sun shirya wani taro na masu ruwa da tsaki akan harkokin siyasa domin tattauna lamurran da suka shafi yaƙin neman zaben. Babban Baturen 'yansanda na shiyyar Funtuwa AC Fiddeko Sani Kura ne ya Jagoranci taron da aka yi a garin Funtuwa a satin da ya gabata. A lokacin taron jami'an hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa na shiyyar tare da wakillan jam iyyun siyasa,da wakilan karamar hukumar da sauran masu ruwa da tsaki ne suka samu halartar taron.
AC Fiddeko Sani kura yace babban makasudin taron shine a tattauna da masu ruwa da tsaki akan kalubalen yakin neman zaben da irin rawar da ake saran masu ruwa da tsakin zasu taka domin cigaba. AC Kura ya ja kunnen jam'iyyu da yantakara game da yin amfani da yan bangar siyasa a tada hargitsi, ya kuma ce jami an a shirye suke suyi aiki da masu ruwa da tsakin don tabbatar da zaman lafiya a lokacin yakin neman zaben.
A nasu bangaren Baturen zaben na shiyyar Funtuwa Mohammed Bashir Musa yayi kira ga jam'iyyun da 'yan yakarar da su gudanar da kamfe abisa dokar zaben, watau, "electoral act" inda yace ofisoshin hukumar zaben zai tafiyar da aikinsa abisa doka da oda. Sannan yayi fatan cewa za a hada hannu wuri guda domin cin nasara.
Wakilin shugaban karamar hukumar Funtuwa Alh Lawal Sani yace karamar hukumar a shirye take tayi aiki da jami'an tsaron da na hukumar zaben a wajen tabbatar da adalci a tsakanin jam'iyyun siyasa. Su ma wakillan ƙungiyoyin matasa da na jam'iyun da na 'yan takara duk sun sha alwashin bayar da hadin kai domin ganin an samu nasarar wannan babban aiki dake tafe