ZA'A ƘARA INGANTA HARKOKIN WALWALAR ALƘALAI DA SAURAN MA'AIKATAN KOTU A JAHAR KATSINA - CJ Danladi

ZA'A ƘARA INGANTA HARKOKIN WALWALAR ALƘALAI DA SAURAN MA'AIKATAN KOTU A JAHAR KATSINA - CJ Danladi
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Anyi kira ga Alƙalan kotunan shari'ar musulunci akan su zama wakillai na gari ta fuskar shari'a a wajen gudanar da aiyukan su kamar yadda doka ta tsara. Babban Jojin Jahar Katsina Mai Shari'a Musa Danladi Abubakar yayi wannan kiran a yayin da ya kai wata ziyarar bazata a wasu kotuna acikin garin Katsina. Kotunan da Babban Jojin ya kaiwa wannan ziyarar bazata sun haɗa da Babbar kotun Majistare ta ɗaya da ta biyu, ta uku da ta huɗu, da kuma Babbar kotun Shari'a ta ɗaya da ta biyu. 
Kamar yadda Babban Jojin yace a lokacin kai wannan ziyara, anyi ta ne da nufin ganin irin halin da kotunan suke ciki tare da tabbar da cewa ana gudanar da shari'u acikin hanzari tare da tabbar da yin adalci. Babban Jojin wanda ya nuna farin cikin shi akan irin yadda yaga ana tafiyar da harkokin kotunan, ya ƙara yin kira gare su da su ƙara ruɓanya abubuwan da suke yi domin ganin an ƙara martaba harkokin shari'a. Kazalika, Mai Shari'ar ya ja kunnen su akan su kiyaye zowa wajen aiki a makare ko tashi ba akan lokaci ba tare da yin sakaci a wajen gudanar da aikin su. Har'ila yau, ya tunasar da Alkalan kotunan akan bukatar da ake akwai na yin shiga ta kamala alokacin da zasu shiga kotu. Babban Jojin Mai Shari'a Musa Danladi ya tabbatarwa Alƙalan cewa, akwai shirye-shiryen ƙara ingantaka jin daɗi da walwalar Alƙalan don ganin an kyautata rayuwarsu ta yau da kullum don maido da martabar harkokin shari'a.
Mai Shari'a Musa Danladi Abubakar ya ƙara yin kira ga alkalan kotunan shari'ar musuluncin da su ƙara duƙufa wajen neman ilmin addinin musulunci don ƙara basu damar gudanar da aikin su na alƙalanci kamar yadda ya kamata.
A nasu sashen, Alƙalan da aka ziyarta sun nuna farin cikin su akan wannan ziyara ta bazata da Babban Jojin ya kai masu, wadda suka nuna cewa, ta ƙara masu ƙwarin gwiwar gudanar da aiyukan su. Saidai kuma Alƙalan sun miƙa bukatansu na neman a ƙara wadata su da kayan aiki kamar su kujeru da tebura da sauran kayan aikin. Nan take Babban Jojin ya umarci Babban Magatakar Babbar Kotun Jahar da ya samarwa da Alƙalan kayan aikin da suke bukata domin ganin aiyukan su na tafiya kamar yadda ya dace.
Daga cikin waɗanda suka rufawa Babban Jojin baya a wajen kai wannan ziyarar bazata sun haɗa da Babban Magatakardar Babbar Kotu Jahar Barista Nuraddeen El Ladan, Darakta dake kula da shigar da ƙara Barista Amina sai kuma Daraktan dake kula da harkokin sadarwa tare da hudda da jama'a Alhaji Musa Usman

Post a Comment

Previous Post Next Post