'YANSANDA SUN CAFKE 'YAN FASHI DA MASU GARKUWA DA MUTANE A JIGAWA

YANSANDA SUN CHAFKE 'YAN FASHI DA MASU GARKUWA DA MUTANE A JIGAWA

Daga Umar Akilu Majeri, Dutse

Rundunar yansanda reshen jahar jigawa ta samu nasarar danke wasu gungun mutane da ake zargin aikata fashi da makami, garkuwa da mutane da satar motoci da Babura da suka addabi Al,ummar jahar jigawa da kewaye .

Kwamashinan yan,sandan jahar jigawa Emmanual Ekot Effiom ya tabbatarwa manema labarai hakan a tsakiyar wannan mako a lokacin da yayi baje kolin wadanda ake zargin. 

Cikin wadanda aka damƙe harda wani tsoho da yake ajiye mutanen da aka sato agidan shi da Kuma wani matashi da yake sayo masu abinci da Kuma wasu matasa da suke safarar tabar wiwi acan yankin karamar Hukumar Ringim ta jahar ta jigawa.

Sauran sun haÉ—a da wani matashi Mai suna Mustapha shehu Dan shekara 33 wanda ake zargin yana aikata fashi da makami da Kuma Mansur Abdullahi Mai shekara 22 wanda akafi sani da yaro yaro bisa zargin yin garkuwa da mutane..

Kazalika, akwai Ali da ake yiwa laqabi da Baba uban jumurɗa ya kuma tabbatar cewar shi ma anayin satar mutane dashi domin ya taɓayi ajahar Katsina.

Sai Kuma wani matashi wanda shekarun shi basu wuce talatin ba mai suna Ali Adamu da aka kamashi da laifin satar mota kirar Honda mallakar wani Dan jarida. Ana kuma zargin Alhassan ya,u Mai shekaru 45 bisa laifin satar mutane yayin da Uzairu Adamu Mai shekaru 21 da abokinsa Zaidu Galadima mai shekara 22 da aka kama su da zargin safarar tabar wuiwui kimanin buhu goma da Rabin buhu.

An kama wani mai ruwan fulani mai suna Muhd Bello da laifin satar mutane . 

Tuni dai aka miƙa matasan biyu da ake zargi da safarar tabar wiwi ga Hukumar NDLEA domin cigaba da bincike tareda tarin buhunan tabar amatsayin shaida yayinda sauran masu laifin aka ingiza qeyarsu zuwa sashin bincike na farin Kaya na yansanda dake jahar jigawa domin tsaurara bincike

Post a Comment

Previous Post Next Post