WASU AYYUKA DA GWAMNA MASARI YAYI DA ZA'A RIƘA TUNAWA DA SHI BAYAN YA BAR MULKI

WASU AYYUKAN DA GWAMNA MASARI YAYI DA ZA A RIKA TUNAWA DA SHI BAYAN YA BAR MULKI

Daga Taskar Labarai 

Hakika lokacin da gwamnatin APC ta karbi mulki ta tarar da tarin matsaloli, faduwar darajar Naira, raguwar kudin shiga da kuma karancin sanin makaman aiki.  Miyagun masu ba da shawara da miyagun 'yan fada, wadanda suka jefa gwamnatin cikin matsalar da har yanzu ba ta fita ba.
Duk haka akwai abubuwa da yawa da tarihi zai tuna da gwamnatin Alhaji Aminu Bello Masari a kan su.
1. Aikin Ruwa: Gwamnatin ta kashe kudi, kuma za a cin gajiyar aikin ruwa sosai da aka yi a Ajiwa Dam da kuma na garin Danja da jawo ruwa daga Dam din Zobe zuwa cikin garin Katsina. 
2. Gidan Gwamnatin Katsina na Abuja: Katafaren ginin Katsina House da ke Abuja, aka sake gyaran shi da chanza masa fatali. wanda zai yi shekaru yana samar wa da Jihar kudin shiga.
3. Katafaren ginin mazaunin dindindin na Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Katsina: Daga mutum ya shigo Katsina daga Kano, wannan ginin ne zai fara yi masa maraba.
4. Katafaren ginin dindindin na ofishin SEPA, wanda Alhaji Isah Barda ya tabbatar an kammala. Ginin yana kusa da FCE Katsina. 
5. Ginin gidajen da ke kusa da asibitin FMC Katsina: An kammala har an fara shiga.
6. Gyaran gidan Gwamnatin Katsina da ke Legas, wanda yana iya samar wa da gwamnatin Katsina kudin shiga. 
7. Ginin bangaren makarantar koyon aikin gona da ke layin Minista na Jami'ar Umaru Musa 'Yar'adua: Duk da yake yana da wahala a fara amfani da shi har su bar mulki, amma an ci karfin aikin. Ko wa ya kammala aikin, za a ce Gwamna Masari ne ya fara.
8. Ginin wajen taro na People's Square, wanda yake kallon gidan gwamnati. Zai iya zama wajen taro har tsawon lokaci.
9. Ginin Asibiti na garin Musawa da gyaran sauran asibitocin a kusan kowace shiyya ta Sanata a Jihar. 
10. Ginin hanyoyin karkashin kasa na Kofar Kaura da Kofar Kwaya da kuma hanyar sama ta GRA. Wadannan hanyoyin sun zama abin kallo da sha'awa a garin Katsina. Za kuma su zama wajen bude ido ga 'yan'uwanmu na karkara in sun shigo birnin Katsina. 
11. An gina hanyoyi daban-daban, wadansu shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bude su da kansa. 
12.za a tuna shi da Gina hanyoyin Ruwa da suka cetar da rayuwa da dukiyoyi masu yawa.wanda a shekarar 2022 anyi ambaliyar ruwan da ba a taba gani ba a kasar nan. Amma katsina tayi sa ar manyan maguda nan ruwa da abin bai shafi jahar ba.
14. Za a rika tuna gwamnatin da hadin kai da aiki tare da aka samu tsakanin shi da mataimakin shi.Alhaji Mannir yakubu.mataimakin da ya shekara 8 a tarihin jahar katsina. 
15. Za a tuna shi da cewa a lokacinsa ne, Alhaji Idris Tune yake Shugaban ma'aikata na Jihar Katsina, kuma ya inganta tsarin aiki da sanya cancanta a gaban aiki. A kan haka aikin na gwamnatin ya inganta.
14. A lokacinsa ya zabi mafi karancin shekaru, Alhaji Malik Anas a matsayin Akanta-Janar, , kuma ya kawo kwarewa, da aiki tukuru da ya canza fasalin tsarin sarrafa kudin Jihar.
15. Za a tuna shi da Gwamna mai dattaku, wanda kuma ba a taba samunsa da hada kai da dan kwangila ba, ko dai a yi kashe-mu-raba, ko a kara masa sifili a kudin aiki, ko cikin ribar da aka samu a debo a kawo masa.
Wannan kadan daga cikin abubuwan da muka tattara ne. Za mu cigaba akan ayyukan Alheri da za a tuna gwamnatin Masari.
A nan gaba za mu kawo maku wasu daga cikin kurakurai da nakasun da aka samu a gwamnatin a ilmance, kamar yadda shi ma muka tara.


Post a Comment

Previous Post Next Post