Sarkin Musawa ga manoma : KU ADANA AMFANIN GONAR KU
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Anyi kira ga manoma musamman na yankin qaramar hukumar Musawa da su adana amfanin gonar da suka noma a wannan shekarar kada su yi saurin fiddawa don sayarwa. Sarkin Musawan Katsina Hakimin Musawa Alhaji Sagir Abdullahi Inde ne yayi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da wakilin ASKGLOCNEWS.
Sarkin Musawan yace, "a irin yadda wannan damana tayi albarka kuma aka samu amfanin gona bakin gwargwado duk da wasu 'yan matsalolin rashin tsaron da ake fuskanta a wasu wuraren, kada manoma suyi saurin fitar da kayan noman su cikin sauri, domin akwai masu irin wannan ƙuduri. Wasu na ganin ko don saboda zasu yiwa 'ya'ya aure ko wani abu makamancin hakan. Yana da kyau a natsu a ga inda aka sanya gaba kafin fara fitarwa a kasuwa. Masu irin wannan can tunani yana da kyau su nemi wata sana'ar da zata sama masu kudaden shiga amma su adana kayan abincin su"
Hakimin wanda yace, lallai akwai wasu kayan amfanin gonar da ake nomawa don sayarwa, to ko su yayi nuni da ayi taka tsan-tsan kafin kaiwa kasuwar.
"Yanzu dai damana tana yi mana bankwana, to tunda Allah yasa yankunan mu akwai wuraren noman rani, to tun yanzu yakamata a fara shirye-shirye akan haka. Manomi yasan abin da zai shuka don samar da kudaden shiga. Sannan kada mu manta da noman shinkafa da sauran irin su, hakan zaisa wata rana aka riƙa kwatanci da mu ta wajen fitar da kayan maimakon shigowa da su.
Ssrkin Musawan yayi kira ga gwamnati da ta cigaba da shigowa don tallafawa manoman musamman ta hanyar samar masu da hanyoyin kasuwancin abin da suke nomawa