SAKATAREN GWAMNATIN JAHA KATSINA YA ZAMA MAGATAKARDAN HAUSA NA FARKO
Daga Ahmed Kabir S/Kuka a Katsina
Kamar yadda Sarkin yace, shi da sabon Magatakardar ba baqin juna ba ne domin sunyi aiki tare musamman a lokacin mulkin marigayi Umar 'Yar'aduwa wanda shi Alhaji Muntarin ya koyar da sarkin harkokin siyasa a lokacin da marigayi Umarun ya haxa su. Sarkin ya kara da cewa, "ba ni ba, duk wanda ke wajen nan yasan wane ne Alhaji Muntari ta fuskar rikon amana da fadin gaskiya tare da jajircewa a wajen aiki. Sannan mutun ne mai dattaku, wanda ire iren waxannan abubuwa yake sa muna bayar da sarauta ga mutane".
Dokta Farouk ya cigaba da cewa, ba Alhaji Muntari wannan sarauta zai kara xaga martaba Hausa da Hausawa a duniya baki xaya domin yasan Allah ya bashi hikimomin da zai yi hakan.
Kafin dai a bashi wannan matsayi a masarautar ta Daura, da ma can masarautar Katsina ta bashi watw sarautar wadda can ma shine na farko da aka ba wannan sarauta wadda za'a iya cewa ya gaje ta tun daga Kakanni kafin ta shigo masarauta a wannan lokacin, wato, sarautar Madugun Katsina. Da yake jawabi a wajen wannan qwaryaqwaryan bikin naxi, Gwamna Masari ya mika godiyarsa a madadin al'ummar Jahar bisa ga wannan karramawa da aka yiwa Sakataren gwamnatin Jahar
Haka shima wanda aka naxan, bayan godiya ga sarkin ya kuma tabbatar da cewa zaiyi iya kokarin shi na ganin ya sabke wannan nauyi da Allah ya aza mashi. Shi dai Alhaji Muntari Lawal wanda aka haifa acikin qoquwar cikin birnin Katsina yayi aikace-aikace a wurare da dama. Sannan ya shahara a fagen siyasa wadda ta kai shi har ga rike mukamin Babban Daraktan yakin neman zaben Gwamna Masari a shekarar 2015 da kuma 2019 duk kuma Allah ya bada nasara akan waxannan zabuka. Har ila yau, kafin zama Sakataren gwamnatin jahar, ya riqe babban Sakatare a gidan gwamnatin Jahar, daga bisa ya koma shugaban ma'aikata na gidan gwamnatin inda daga nan ya zama Sakataren gwamnatin Jahar.