MATASA KE JAN RAGAMAR SIYASAR WANNAN LOKACI - Abba D. Safana

MATASA KE JAN RAGAMAR SIYASAR WANNAN LOKACI  - Abba D. Safana
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
A lokuttan baya ana yawan cewa, matasa ne ke ƙashin bayan ci gaban al'umma musamman a duk lokacin da aka ce harkokin siyasa sun matso, amma a ƙarshe sai matasan su zamo koma baya a harkokin mulki sai nadiran-nadiran. Amma wannan lokacin a iya cewa, abubuwa sun canza musamman a wannan ƙarni na 21 wanda ya zamo matasan sun zaburo ta fuskoki daban-dabam.
A hirar shi da wakilin ASKGLOCNEWS, Babban Daraktan ƙungiyar matasan nan mai suna "Youth to Youth(Y2Y)" wato, 'Daga matasa zuwa matasa' don ganin an zabi dan takarar kujerar Gwamnan Jahar Dokta Dikko Radda tare da Mataimakin shi Faruk Jobe a zaben 2023 mai zuwa a ƙarƙashin jam'iyar APC, Alhaji Abba Dayyabu Safana ya fara da baiyana kadan daga cikin tarihin ƙungiyar wadda yace an kafa tun shekarar 2014 a lokacin yaƙin neman zaben Mai girma Gwamna Aminu Bello Masari.
Kamar yadda Babban Daraktan ƙungiyar yace, a wancan lokaci sunyi amfani da dabarun wayar da kan matasa akan harkokin ita kanta siyasar da kuma yadda zasu gudanar da zabe. "Allah cikin ikon shi yasa ƙungiyar ta taka muhimmiyar rawa har kuma Allah ya sa aka ci zaben 2015. Haka ma abin ya faru a zaben 2019. To sai muka ga tunda har akwai wata rawar da muke takawa, yasa a wannan karon ma muka sake maido da ƙungiyar tunda da ma ba mutuwa tayi ba".
Alhaji Abba Safana ya ƙara da cewa, ƙungiyar Y2Y na da rassa tun daga matakin rumfa, mazaɓa, ƙaramar hukuma har zuwa ga Jaha. "Ƙungiya ce wadda ta taso da tsari da manufofi tun daga farkon kafuwarta har zuwa yau, domin ko a wancan lokacin Ɗantakarar mu na yanzu, wato, Dokta Dikko Raɗɗa yana daga cikin uwaye na wannan ƙungiya." Sannan lokacin da Mai girma Gwamna Masari ya ci zabe bai manta da wannan ƙungiya ba, domin ya tallafawa wasu daga cikin membobin ta. Har'ila yau, Ɗanmajalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dutsinma na yanzu yana cikin wannan ƙungiya kuma matashi ne kamar yadda shi kan shi ɗan takarar yake matashi".
A hirar da muka yi da shi mai tsawon minti 30 wadda za'a ganta a tashar mu ta You Tube acikin shirin 'YADDA KA ZUBA HAKA ZAKA KWASHE', Babban Daraktan yace, "idan Allah yaba ɗan takarar mu Dikko Umar nasara muna da yaƙinin zaiyi abin da ya dace ga Jahar Katsina,musamman ga matasa. Shi yasa kaji sunan ƙungiyar daga matashi zuwa matashi". Alhaji Abba Dayyabu yayi nuni da cewa, a yanzu matasa ne ke jagorancin harkokin siyasar wannan lokacin duba da irin yadda suka jajirce ake damawa da su musamman a wajen neman kujerun mulki a matakai daban-dabam.
Jagoran Æ™ungiyar sai yay kira ga masu sukar 'yan takarar da cewa, maimakon yin É“atanci ga wani É—an takara kamata yayi mutun ya fito ya tallata na shi muddin yasan yana da abin da zai tallata shi ba ma kamar ta kafofin sadarwar zamani da wasu ke amfani da su don aibata wasu. "Duk wanda kaji yana aibata wani É—antakara to lallai yasan bashi da abin da zai tallata na shi ne". 

Post a Comment

Previous Post Next Post