Martani : TARBIYA DAGA GIDA TAKE FARAWA

Martani :TARBIYA DAGA GIDA TAKE FARAWA - Al Amin Isa

Ana samun Dattaku a wurin yaro, ana samun Dattaku a wurin babba. Kuma yawan shekaru basune kesa a cema mutum Dattijo ba. Akwai wasu halaye da yan’ Adam ke dubawa wurin mutum kaji sunce ai wane Dattijo ne, ko da kuwa yanada karancin shekaru a duniya. 
Na ga wani video dake yawo akan social media wanda Ahmad Babba Kaita ke magana a taronsu na Jibia daga baya kuma naga yayi rubutu a shafinshi. Ahmad Babba Kaita yana cikin wadanda mukayi gwagwarmayar murkushe PDP tun yana CPC har akayi maja muka dawo APC.  Tsakaninmu akwai fahimta, akwai mutuntawa da girmama juna. A cikin APC kuma har yanzun munada yawa wadanda mukeda irin wannan alakar dashi, kamar mutane irin Maiwada Dammallam da Abdullahi I. Mahuta da Bishir Gambo, etc kuma Bahaushe nacewa ko lahira wani yana cin albarkacin wani. Wannan yasa nake ganin koda Ahmad bai kalli shekaru da girman kujera dakuma alaka da sukayi a baya da Gwamna Masari ba, to ko domin mu dake tare dashi, zaiyi mashi ragowa. A tarbiyarmu ta musulunci dakuma al’adar Hausa-Fulani muna tashi daga gidajenmu da horon daga gun iyayenmu na mu girmama wanda yake gabanka a shekaru, dakuma biyayya ga Shugabanni. Irin wannan tarbiyar tasa a al’ada ko a cikin gidajenmu muke cewa Babban Wa Uba. Akwai wasu kalamai  da dukk mutum da Allah yabashi matsayi na Shugabanci ba zai so jama’a suji yana alakantuwa dasu ba balle ace shine ke furtasu. Yakamata ka gane kai Sanata ne a Najeriya, nasan kuma kasan matsayinka a order of protocol na kasarnan.
Ita kujerar da kake akai, kuma kake yin takara kanta a 2023 sunanta Majalisar Dattawa, ashe kuwa wanda har yake amsa sunan Dattijon Najeriya to yakamata aga halin Dattaku tare dashi, ko da shekarun shi basu kai na tsufa ba. Babu inda Dattijo ke furta irin wadannan kalaman da ka keyi. Domin babu dattaku cikin irin wadannan kalaman. Naga cikin rubutun da kayi kana kokarin ka rarrabe tsakanin Dattijo da Tsoho, domin kayi justifying kalamanka akan Gwamna Masari. To abin tambaya anan shine, idan mukayi la’akari da matsayinka na Sanata (Dattijo a Najeriya) kai a wanne mataki zamu ajiyeka kenan? Domin Dattijo baya zagi, ko furta kalaman da jama’a sun san basuda alaka da Dattijo, ko da yaushe ana samun Dattijo da nuna halin girma, dakuma gabata, ta hakane wadanda ke biye dashi zasuyi koyi dashi. 
Na tabbatar da kaima ba zakaji dadin wani yahau drum yayi maka irin wadannan kalaman ba, ko da tsaranka ne balle wanda ka girma ko kake gabanshi a matsayi.  Shi dai Gwamna Masari baya takara ko wacce iri a 2023, yanzun wa’adin mulkinshi baya wuce sauran watanni. Inaga yanzun abinda jama’a ke bukatar ka mayar da hankali akai shine, bayani akan ita sabuwar Jam’iyyar ka da kuma qualities na dantakararku a PDP, wanda zai sanya masu zabe su ajiye namu na APC su zabe ku. Muna bukatar kafito ka gaya muna a yanzun minene yachanza daga shi Yakubu Lado daka bamu labarinsa chan baya? Wadanne qualities ne sukayi endearing naka ga Yakubu Lado yanzun? Muna bukatar ka haska muna Dikko Radda da Yakubu Lado da hujjoji kwarara da jama’a zasu gamsu su ajiye maganarka akan Yakubu Lado a 2019. 
Naga cikin rubutunka kayi maganar abinda jama’a yakamata su rinka yiwa tsoffin Gwamnoni irin Mallam Ummaru Musa amma sai nayi mamaki naga ka tsallake Gwamna Shema ka diro kan Gwamna Masari, shin shi Gwamna Sheman baya cikin wadanda kakeso ayima Addu’a ne? Tunda shi Gwamna Masari kace babu Addu’a tsakaninku to shi Gwamna Shema fa? Ko shima har yanzun akwai jidalin kanshi shiyasa kayi hikima ka zagayeshi domin bakason jama’a su gane abinda ke zuciyarka kanshi? 
Kanada damar da zaka soki Gwamnatin Masari, mu kuma zamu iya kareta mu baka amsa amma idan sukar mai tsafta ce. Zan kuma so ace ka koma yin objective criticism domin mu kamar tallah ce zakayi muna tunda dole zamu fito mu kare da hujjoji da zasu gamsar da jama’a, amma Ahmad bashi yiwuwa mudawo a shekarunmu mu zama yan jagaliya muna zagin juna bisa social media. Ni a yanzun ina ganin banyi ma kaina adalci ba idan na mayar maka da martani a irin yanayin dakai ka rufe ido kaci mutuncin Gwamna Masari batare da kayi la’akari da irin mutuncin da ke tsakaninmu dakai ba muda muka sanka kuma muke tare dashi.

Post a Comment

Previous Post Next Post