HUKUMAR KIYAYE HADDURA TA MAYAR DA KUDADE GA MAGADA A KATSINA

HUKUMAR KIYAYE HADDURA TA MAYAR DA KUDADE GA MAGADA A KATSINA 
Daga Sa'adu Saulawa
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa reshen jahar Katsina ta mayar da kudade sama da naira miliyan uku ga iyalan wadansu fasinjojin da suka rasa rayukansu asanadiyyar hadarin mota a shiyyar Funtuwa. Wadannan kudade da jami'an hukumar kiyaye hadurra ta kasa reshen Funtuwa suka mayar tun can farko sun adana su bayan rasuwar Fasinjojin da hadarin ya rutsa dasu kuma suka nan take. Adana kudaden ya biyo bayan saurin kai dauki da jami'an hukumar suka yi a lokacin da hadarin afku inda suka yi tozali da wadannan kudade kuma suka dauke su don kaucewa fadawa a hannun É“ata gari acikin sauran jama'a masu kawo gudunmuwa a lokacin da wani haÉ—ari ya faru. 
Shugaban hukumar ta kasa reshen Jahar Katsina AS Tanimu ne ya mika kudin ga iyalan fasinjojin da suka rasun a wani kwarya-kwaryan buki da aka yi ofishin shiyyar Hukumar dake Funtuwa. Shugaban hukumar har ila yau ya bukaci direbobi da su rinka tuki da kula domin kare rayuka da dukiyoyin alumma. AS Tanimu yace, tuni ya rubuta ma babban ofishin hukumar dake Abuja cikakken rahoto akan irin rikon gaskiya, kishin kasa da nagarta da jami an suka nuna na dauka tare da adana waÉ—annan kudade don hannanta su ga magada. Har wayau, Shugaban yace nan bada  jimawa ba za'a karrama wadannan jami'ai domin wannan gaskiya da nagartar da suka nuna. A na shi bayanin, Shugaban hukumar na shiyyar Funtuwa IS Abdulkarim ya bayyana bukatar direbobi su rinka bin dokokin hanya kuma su riÆ™a kauracewa yin tukin  ganganci da shan kayan maye. 
Wasu daga cikin Iyalan mamatan sun yaba da kwazo,gaskiya, da rikon amana tare da nuna nagarta da jami'an hukumar kiyaye hadurra a shiyyar Funtuwa abisa yadda suka adana wadannan kudade da su kayi. Sun kuma yi kira ga sauran ma'aikata dasu yi koyi da hali irin wadannan jami'ai. 

Post a Comment

Previous Post Next Post