HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA ZA TA FARA KAI MASU SON ZUWA AIKIN UMRA

HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA ZA TA FARA KAI MASU SON ZUWA AIKIN UMRA 

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 

Nan bada jimawa hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Katsina karkashin jagorancin Babban Daraktan ta Alhaji Sulemain Nuhu Kuki tana cigaba da shirye-shiryen fara jigilar masu zuwa Umra a kasa mai tsarki.
Kamar yadda Babban Daraktan ya shaidawa ASKGLOCNEWS a ofishin sa dake cikin babban birnin jahar, Alhaji Sulemain Nuhu Kuki ya ce, tun lokacin da ya shigo jagorancin wannan hukuma ya fara wannan tunani wanda kuma ya samu goyon bayan abokan aikin sa akan cewa, yana da kyau a fara jigilar masu son zuwa don yin aikin Umra a hukumance maimakon aiyukan Hajji kamar yadda aka saba a duk shekara. Ko zuwan wannan aikin Hajji na 2022 da Allah ya bamu ikon zuwa,mun tuntuɓi masu ruwa da tsaki acan ƙasar Saudiya. Da ma anan gida, lokacin da muka rubutawa Mai girma Gwamna Masari akan wannan shiri, bai tsaya wata-wata ba ya amince mana. Kuma yace zai bayar da duk wata gudunmuwar tamkar irin wadda yake bada a lokacin aiyukan Hajji. Tuni dai muka yi magana da wasu kamfanonin da ke gudanar da wannan aiki domin ganin cewa mun samu nasarar cimma wannan ƙuduri na mu".
Babban Daraktan ya ce, batun samar da jiragen da zasu aiwatar da wannan aiki ba matsala ba ce, tunda akwai kamfanin da yake na gida ne, wato, Max Air wanda yake a shirye a kowane lokaci aka tuntube su. 
   Da muka tuntuÉ“i wasu masu ruwa da tsaki akan wannan harkar da kuma wasu masu son zuwa wannan aikin ibada, sun nuna farin cikin su akan wannan babbar nasara da kuma tarihi da wannan hukuma zata kafa, don wannan shine karon farko da za'a tafi wannan aiki a Æ™arÆ™ashin hukuma. Hakan zai Æ™ara baiwa masu zuwan Æ™warin guiwa da kuma kawai da fargaba a irin wasu matsalolin da ake fuskanta akan wannan aiki. 

Post a Comment

Previous Post Next Post