Dangane da canjin kudi: TA LEƘO ZA TA KOMA GA BABBAN BANKIN NAJERIYA

Dangane da canjin kudi : TA LEƘO ZA TA KOMA GA BABBAN BANKIN NAJERIYA  
 
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele ya bayyana cewa bankin zai sauya fasalin kudin kasar a ranar 15 ga watan Disamba, 2022, amma sai ga gwamnatin tarayya ta ki amincewa da shirin a ranar Juma’a 28 ga Oktoba 2022 
Wannan ƙin amincewa ya biyo bayan baiyana haka da Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare ta Kasa, Zainab Ahmad, wadda ta yi watsi da batun shirin, ta ce idan aka aiwatar da shi to zai yi illa ga kasa da tattalin arzikinta. 
Minista Zainab, wacce ta yi tsokaci kan manufar yin haka yayin da ta ke amsa tambayar da Sanata Opeyemi Bamidele yayi a zaman kare kasafin kudi na 2023. Ta kuma gargadi CBN kan sakamakon da ka iya tasowa daga baya.
Sanata Bamidele wanda a cikin tambayarsa ya shaida wa Ministar Kudi cewa kwanaki biyu bayan sanarwar da CBN ya fitar, an fara jin tasirin hakan kan darajar Naira zuwa Dalar Amurka, ya ce, “Kwana biyu kacal da sanar da manufar, darajar Naira zuwa Dalar Amurka ta tashi daga N740 zuwa N788 akan dalar Amurka sakamakon gaggawar musayar Naira zuwa kudaden kasashen waje,ba ma kamar dala.
“A gare ni, manufar na iya zama kyakkyawan tunani, amma lokacin aiwatar da ita ne bai yi ba duba da cewa hakan zai zubar da darajar Naira zuwa har N1,000 a kan dalar Amurka kafin ranar 31 ga Janairu, 2023 don aiwatar da manufar gaba ɗaya..”
Yayin da take amsa tambayar, Ministar ta ce ba ta da masaniya kan manufar, inda ta ƙara da cewa a kafafen yada labarai kawai ta ji sanarwar. Ta ƙara da cewa, “Ya ku Sanatoci masu girma , ba a tuntube mu a ma’aikatar kudi daga CBN ba game da shirin sake fasalin Naira kuma ba za mu iya cewa komai dangane da cancanta ko akasin haka ba .
“Duk da haka a matsayi na ta ƴar Nijeriya da ke da damar kasancewa a kan gaba a harkokin kasafin kudin Najeriya, manufar da aka fitar a wannan lokaci, tana nuna mummunan sakamako kan darajar Naira ga sauran kudaden waje. “Duk da haka, zan yi kira ga wannan kwamiti da ya gayyaci Gwamnan Babban bankin na CBN domin samun cikakken bayani game da cancantar manufofin da aka tsara da kuma daidai ko akasin haka na aiwatar da shi a yanzu.

Post a Comment

Previous Post Next Post