DA KASAFIN NAIRA BILYAN GUDA NA TARAS A SMEDAN NA BARTA DA NA BILYAN 28 - Dikko Radda

DA KASAFIN NAIRA BILYAN GUDA NA TARAS A SMEDAN NA BARTA DA NA BILYAN 28 - Dikko Radda
Daga Jamilu Hashim Gora
 Tsohon shugaban hukumar bunÆ™asa Æ™anana da matsakaitan masana'antu, É—an takarar kujerar Gwamnan jihar Katsina a zaÉ“en 2023 Æ™arÆ™ashin jam'iyar APC Dokta Dikko Radda, ya ce, ya taka muhimmiyar rawa wajen farfado da hukumar Bunkasa Kanana da Matsakaitan Masana’antu ta Kasa a lokacin da ya karbi ragamar mulkin hukumar a 2016 
Ya cigaba da cewa, ya tadda hukumar ta SMEDAN a kan kasafin kudi Naira biliyan daya da rabi, amma a watan Afrilu na shekarar 2022 lokacin da yayi murabus, kasafin kudin na hukumar a shekarar 2022 ya kai Naira biliyan Ashirin da takwas, wanda a tarihin hukumar ba a taba samun irin shi ba. Ya kara da cewa, zai bude hukumar Kanana da Matsakaitan Masana’antu idan Allah ya bashi nasara domin taimakawa masu kananan sana’oi da kuma farfado da bankunan bada jari a Jahar Katsina. A karshe ya bada tabbacin cewa yana da tsare-tsare wanda zasu farfado da tattalin arzikin jihar Katsina wanda kananan sana’oi zasu samu habbaka su kai ga matakin gaba.
ÆŠan takarar ya baiyana haka ne a lokacin da Kungiyar yan kasuwa ta jihar Katsina suka kawo ma shi ziyara tare da nuna amincewar su ga takarar da yake yi a wani zama da ya gudana a tsakanin su a gidan shi dake Batagarawa, a ranar Litinin 18 ga Oktoba na 2022. 
Shugaban Ƙungiyar yan kasuwa ta jihar Katsina Mujittafa Lamis Gafai, ya shaida ma ɗan takarar cewa sun amfana da gwamnatin APC a matakai daban-daban da kuma shirye-shirye da gwamnati ta bullo da shi. A sabili da haka zasu bada cikakken goyon bayan su da kuma kira ka yan kasuwa da su marawa jam'iyyar APC baya a zabukan 2023.
Alhaji Hamisu Dutsi, Shugaban Kungiyar 'yan kasuwa na karamar hukumar Dutsi, ya shaida cewa zabar Dokta Dikko Radda, zabi ne wanda 'yan kasuwa ba zasu taba yin da na sani ba.'Yan kasuwar sun shaida a lokacin Dikkon yake Shugaban Hukumar Kanana da Matsakaitan Masana’antu ta Kasa (SMEDAN), ya bullo da shirye-shirye wanda 'yan kasuwar suka amfana da su, kamar "Survival Fund" yiwa 'yan kasuwa 6,606 rijista kyauta, da kuma tallafi na Naira dubu talatin (N30,000) wanda masu harkar sufuri suka samu a shekarar 2020. Ya tabbatar da cewa zasu mara mashi baya a aniyar shi ta zama gwamnan jihar Katsina.


Post a Comment

Previous Post Next Post