Da dumi dumi YAN BINDIGA SUN KASHE TSOHON SHUGABAN ƘUNGIYAR MALAMAI DA WASU MUTUN 4 A KATSINA

Da dumi dumi YAN BINDIGA SUN KASHE TSOHON SHUGABAN ƘUNGIYAR MALAMAI DA WASU MUTUN 4 A KATSINA
Labarin dake shigo mana a yanzun nan na cewa, wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari a kauyen Bugaje inda suka kashe tsohon shugaban kungiyar malamai na karamar hukumar Jibiya tare da wasu mutane 4 na kauyen Kada dake ƙaramar hukumar Jibiya
Kamar yadda majiyar ta ce, 'yan bindigar da yawan su ya kai mutun 6 wadanda suka zo akan babura 3,sun yi harbin kan mai uwa da wabi har suka kashe wadannan mutane. Sai dai babu rahoton tafiya da wani ko wasu don yin garkuwa.
Karin bayani na nan tafe

Post a Comment

Previous Post Next Post