Da dumi dumi MAI MARTABA SARKIN KATSINA ZAI DAWO GIDA A RANAR LITININ 31 GA OKTOBA 2022

Da dumi dumi MAI MARTABA SARKIN KATSINA ZAI DAWO GIDA A RANAR LITININ 31 GA OKTOBA 2022
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
Kamar yadda wata sanarwa ta fito daga masarautar Katsina Æ™arÆ™aahin kulawar 'Yandakan Katsina Alhaji Sada Muhammad Sada wadda Sarkin Labaran Masarautar ta Katsina Alhaji Ibrahim Bindawa ya baiyana, Mai Martaba Sarkin Katsina Dokta Abdulmuminu Kabir zai dawo gida a ranar litinin 31 ga watan Oktoba na 2022,bayan zaman jinya da yayi a Æ™asar London ta wani É—an lokaci. 

Kamar yadda sanarwar ta nuna, Sarkin zai sabka a filin sabka da tashin jirage a tsakanin ƙasa da ƙasa na Umar 'Yar' adua dake cikin babban birnin Jahar da misalin ƙarfe 10 na safe.
Kazalika, sanarwar tayi nuni da cewa, bayan Sarkin ya fara zuwa gidan gwamnatin jaha, zai biyo ta hanyoyin da aka keÉ“e bisa dalilan aikin gadar sama da ake yi akan shatalai-talai na Bariki. Mai martaba Sarkin zai biyo ta wajen masallacin Bani Kumasi zuwa Kofar Durbi domin haduwa da mahaya dawaki wanda zasu tarbe shi a bisa wata Æ™warÆ™waya Dabar tarba da aka shirya. 

Post a Comment

Previous Post Next Post