Da dumi dumi KWAMANDAN DAJI LANƘAI YA YO GABAS DAGA MALLAMAWA

Rahotannin dake shigo mana a yanzu na cewa, daya daga cikin kwamandojin dajin da suka addabi yankin Jibiya da Batsari mai suna Audu Lanƙai angan shi tare da tawagar shi sun baro maboyar shi dake wajen Mallamawa sun yo Gabas akan babura bayan sallar Azahar kuma har zuwa wannan rubutun ba'a ga sun dawo ba kuma ba'a ji duriyar inda suka dosa ba. 
Kamar yadda rahotannin ke nunawa, ana zargin Lanƙai zai kai hari a daya daga cikin wadannan garuruwan da suka hada da. Kagadama, Magamar Jibiya, Yangaiya, Gangara, Gakurdi ko Bugaje da sauran yankin. Audu Lankai dai na daga cikin manyan 'yan ta'addan da suka addabi wadannan yankuna.
Ko a ranar Asabar sai da maharan suka tare hanya a Magamar Jibiya inda suka tafi da jama'a, har ila yau, a ranar litinin da ta gabata sai da wasu.'yan bindigar suka kai hari a garin Bugaje har suka kashe mutun biyar tare da yiwa wasu rauni. 

Post a Comment

Previous Post Next Post