Da dumi dumi AN JINGINE DOKAR HANA HAWA BABUR DA DARE A JAHAR KATSINA

Da dumi dumi AN JINGINE DOKAR HANA HAWA BABURA DA DARE A JAHAR KATSINA 

Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina 

Gwamnatin Jahar Katsina ta jingine dokar da ta kafa na hana hawan babur da kurkura a duk fadin jahar tun daga karfe 10 na dare har zuwa 6 na safe domin matsalar tsaro da ake fuskanta a Jahar.
Kamar yadda wata sanarwa ta fito daga ofishin Mai baiwa Gwamnan shawara ta kafofin sadarwar zamani Alhaji Aminu Isa ta ce, wannan matakin jingine wannan doka ya biyo bayan ba al'ummar jahar damar yin walwala a lokacin ta ake shagulgula tunawa da ranar haihuwar Cikamakin Annabawa, Annabi Muhammadu(SAW)
Gwamna Masari ya ce, an dakatar da dokar tun daga ranar 14 ga watan Oktoba har zuwa 20 ga watan Nuwamba. Gwamnan yayi kira ga musulmi da suyi amfani da wannan dama domin Æ™ara cigaba da yiwa jahar addu'o'in samun zaman lafiya tare da kasa baki daya. Sannan ya ja hankalin jama'a da su zamo masu bin doka da oda ne  a kowane lokaci. 

Post a Comment

Previous Post Next Post