BA KARƁAR KUƊI NE KE CIN KE CIN HANCI GA ALƘALAI BA HAR DA....... - CJ Musa Danladi

BA KARƁAR KUƊI NE KE CIN HANCI GA ALƘALAI BA HAR DA.... - CJ Musa Danladi 

Daga Kabir Ahmed S/Kuka

Babban Jojin Jahar Katsina Mai Shari'a Musa Danladi Abubakar ya ce, ba wai ba Alƙali kuɗi ba ne ta bayan fage ke cin hanci da rashawa, a'a, akwai sauran abubuwan da idan Alƙali yayi su shi ma cin hanci da rashawa ne. "Ƙin zuwa wajen aiki cikin lokaci, ko ƙin bayar da kofin shari'a a lokacin da aka ɗaukaka ƙara duk hanyoyi ne na cin hanci da rashawa wanda kuma ka iya sanya hukunta alƙali.Babban Jojin ya baiyana haka ne a ranar talata 11 ga watan Oktoba na 2022 a lokacin da ake rantsar da sabbin alƙalan shari'a su 9 a ɗakin taro na Babbar Kotun Jahar Katsina dake kan titin zuwa Daura a Katsina. Mai Shari'a Musa Danladi wanda yayi jawabi mai tsawo na jan hankali ga mahalarta taron ba wai alƙalan ba. "Duk wanda ya shiga fannin alƙalanci tabbas ya shiga cikin wani yanayi mai sarƙaƙiya da yin taka tsan-tsan. Za'a kawowa Alƙali shari'a wadda ba gaban shi aka aikata abin da aka kawo ƙarar ba, amma kuma ace ana so ya yanke hukunci akai, wanda dole ne bayan yayi bincike bisa ga dogaro da ƙwararen hujjoji da shaidu yayi adalci wanda kuma ake sa ran kowane sashe zai gamsu da hukuncin. Saboda muhimmancin tsaron kai da ita kanta shari'ar abu biyu na hawa kan Alƙali. Abu na farko shi ne, ribar da ake akwai ta idan Alƙali yayi abin da ya dace. Sannan abu na biyu wanda kuma yake mai wahala ga mai yin alƙalanci shi ne, canza mashi yanayin rayuwa. "Inda ake zama don yin hira da irin hirar dole ya canza. Duk wani abin da ya sani yana yi na yau da kullum kafin zama alƙali, da zarar ance yau ya zama, to wwjibim shi ne ya canza ba don komi ba sai don kare mutuncin kan shi da ita martar shari'ar. Kazalika, akwai wani abin da yake halal ne, amma sai ya zamo haram ga alƙali. Misali, yayi shari'ar sakin aure kuma ya zagaya ya auri matar. Yin hakan ba laifi ba ne, amma a fannin shari'a abin ya zama haran ga alƙali, domin jama'a ba zasu ƙara yarda da shi, saboda sun ɗauke shi mai adalci ba".Mai Shari'a Musa ya kawo misalai da yawa ciki kuwa har da batun shigar sutura da sauran su. Shi kuwa Alƙalin alƙalan Jahar Katsina Dokta Kabir Abubakar addu'o'in samun zaman lafiya yayi tare da roƙon Allah da ya karya duk wani mai hannu akan matsalolin da ake fuskanta musamman akan batun sha'anin tsaro.Alƙalan shari'ar musuluncin da aka rantsar sun haɗa da, Jamilu Abdullahi Cikin Gida, Nafi'u Rabi'u Usman, Ashafa Abubakar, Hassan Kabir Isma'il. Sauran sun haɗa da Umar Muktar Danjana, Yusuf Lawal Kurungafa, Anas Bara'u, gami da Lawal Dan Asabe da Kabir Al Hassan, waɗanda suke jira tura su kotunan da zasu gudanar da aiyukan su. 

Post a Comment

Previous Post Next Post