ƊAN JAHAR KATSINA NA FARKO DA GOOGLE SUKA GAIYATA ZUWA AMURKA

ƊAN JAHAR KATSINA NA FARKO DA GOOGLE SUKA GAIYATA ZUWA AMURKA

Askglocnews 

Tun farkon shigowar kafafen sadarwa na zamani musamman na sada zumunta irin su 2go,Tawoo da sauran su har zuwa shigowar su Facebook har zuwa yau, an samu shigar matasa akan harkokin yin amfani da waɗannan hanyoyi ta fuskoki da dama. 
Amma ga Shafi'i Alolo ya riƙa amfani da wannan kafa ta wasu hanyoyin daban da ya sha bamban da sauran masu yin ta. Farko, ya fara amfani da wannan kafa musamman a wajen tarurrukan siyasa, domin matashi ne wanda ya rika nuna sha'awar shi a harkokin siyasa. A lokacin mulkin PDP Alolo yayi tallar 'yan takara fiye da yadda ake tunani. Amma sai dai ya ƙi yarda ya nuna goyon bayan shi a wani dan takara in aka debe kujerar Gwamna.
Tun ba'a fara farga da tallar dan siyasa a kafar sadarwa su Shafi'i tare da abokin shi na wannan lokaci Sardauna. Babban abinda ya ƙara sanya mashi kwarjini a tsakanin 'yan siyasar tun a wancan lokaci shine, irin ƙarya da baiyana abinda ba'ayi ba da wasu suke yi Alolo ya kebe kan shi daga wannan tsari. Hatta da hotunan da yake azawa sai na tabbas ba hade-hade ba. Abu yana yi kamar da wasa ko ra'ayi, amma sai ya rike wannan harkar a matsayin sana'a kuma wadda ya ba muhimmanci. Hakan bai sanya shi barin sana'ar shi ta farko ba, wadda har ake yi mashi lakabi da ita, wato, "Alolon Shago". Kazalika, daukakar da ya fara samu musamman daga 'yan siyasa bata sanya shi yin girman kai ko wani abu makamancin haka ba. Bai kuma rabu da abokan huddar shi ba. 
Watakil, irin sanfuri da nau'o'i ko salon yin amfani da wannan kafa wadda abin ya wuce sanya harkokin siyasa, ta kai har da sauran wasu bayanai na fadakarwa ko sanarwa da sauran irin su wanda Alhaji Shafi'i Alolo ya rika yin amfani da su da wannan kafa. Ya kuma rike dokokin yin amfani da kafar wadda har zowa yau babu wanda zaice yayi kuka da shi akan batanci.
Tabbas, wadanda suka kirkiro da wannan hanya ta amfani da wadannan tashoshin sadarwa na zamanin, musamman rumbun aje bayanai wato, Google, sun yi mamakin irin yadda Alolo mai Kamfanin "Mobile Crew" ke tafiyar da harkokin shi. Bisa binciken da suka gudanar, akwai kyawawan hotuna da yake yin amfani da su tun ma lokacin da yake amfani da wayar hannu. Sannan idan bidiyo zai buga, baya ga hoto mai kyau, akwai fitar murya yadda kowa zai ji abinda ake cewa. Har ila yau, bisa ga binciken mu, Alolo yayi amfani da wannan hanya domin taimakon al'umma musamman mabukata ko wadanda suka shiga cikin wani yanayi. Yayi amfani da wannan dama domin sanar da hukumomi abubuwa da dama ciki har da abin da ya shafi batun tsaro. Kamfanin Google bisa ga dukkan alamu sun dade suna bibiyar harkokin Shafi'i wanda hakan yasa ya zamo wani abin alfahari ga al'ummar Jahar Katsina akan cewa, shine matashi na farko mai amfani da kafar sadarwa wanda kuma kamfanin rumbun tara bayanai yayi bincike tare da nazari akan irin yadda yake tafiyar da wannan hanya, abinda yasa har suka gaiyace shi zuwa ƙasar Amurka babbar hedkwatar wannan rumbu. Shafi'i ya bar Najeriya a ranar 9 ga watan Mayu na 2022 inda ya fara yada zango a ƙasar Dubai kamar yadda Google suka tsara mashi wannan tafiya. 
Shin sauran masu amfani da kafofin sadarwar ko akwai wani darasi da za'a ce tafiyar Alolo Amurka bisa gaiyatar Google ta koyar da su idan aka yi la'akari da irin yadda wasu ke gudanar da ita? Wannan ya nuna cewa, ashe duk abinda mutun ya dauka da muhimmanci zai ga sakamakon abinda yake yi? Wane kalubale ke ga tafiyar Alolo Amurka ga 'yan "Social media". Alhaji Shafi'i Alolo dai ya kafa tarihi a ƙarni na 21/22 ta fannin amfani da kafar sadarwar zamani. 

Post a Comment

Previous Post Next Post