ZAMAN 'YAN AREWACIN NAJERIYA A YANKIN KUDU

’Yan Arewacin Najeriya mazauna yankin Kudu sun koka bisa yadda suke zargin an mayar da su abin kashewa da kuma tsangwama a yankin da suke zama.

Shin mene ne gaskiyar wannan zargi kuma ina gaskiyar kirarin da ake yi wa Najeriya da cewa, ’Kasa daya, al’umma daya’?

Ina kuma ’yancin da dokar kasar ta bai wa kowane dan Najeriya na zama a duk inda yake so a kasar bisa doka, ba tare da an cutar da shi ko an nuna masa wariya ba?

Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da wasu ’yan Arewa mazauna Jihar Anambra kan halin da suke ciki a can.

Domin sauke Shirin latsa nan: https://bit.ly/3B9EdgU

Post a Comment

Previous Post Next Post