YAƘIN NEMAN ZAƁE TA WAYO KO CANJIN SHEƘAR SIYASA? Jahar Katsina a ma'auni

A bisa dokar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, wato, INEC, jam'iya ko ɗan takara basu da izinin fita yaƙin neman zabe sai a tsakanin kwanaki 90 na gudanar da zaben a kuma kowane irin mataki. Saɓawa bin wannan tsari ko doka laifi ne da ka iya kawo hukunci wa lau ga jam'iya ko ɗan takarar ko kuma duka biyun. 
To amma ana bin wannan doka ko kuwa akwai masu yi mata karan tsaye ko bin wasu hikimomi da dabarun na kaucewa wancan hukunci? Kun san ana cewa ɗan Najeriya akwai shi da iya hikima da dabara na ganin ya karya doka amma ba za'a iya hukunta shi saboda lalatar da sheda. 
A wannan iskan mai bugawa a kuma lokacin da iska siyasar 2023 ke qoqarin kaɗawa, tuni har wasu jam'iyun ko 'yan takarkarin su sun fara girgiza rassan da zasu haifar da bugawar iskan tun ma kafin lokacin yayi. 
Zamu dubi abubuwan dake faruwa a wasu jihohin inda muka aza Jahar Katsina a matsayin ma'auni domin gano tahakikanin yadda lamarin ke tafiya. Shin ana bin wannan doka ko a'a? Bisa ga abubuwan dake faruwa a tsakanin su 'yan siyasar musamman 'yan takarar da suke jiran lokacin zabe, akwai wasu dabaru da suka bullo da shi wanda yayi kama da yaƙin neman zaɓen su ko kuma jawarcin canjin sheƙar siyasa daga wasu da ake kallo suna da tasirin siyasa, koda yake neman irin wadannan mutane abu ne wanda siyasa ta gaba. A wasu lokuttan ma zaka ga hatta da jam'iyar siyasa mai gwamnati tana irin wannan yunkurin. 
To sai dai abin tambaya akan irin abubuwan dake faruwa a yanzu wanda ɗan takara zaiyi tafiyayya zuwa wani wuri yasa a tara mashi jama'a yayi masu jawabi irin na yakin neman zabe, sai in anyi magana sai ace, ai yawon godiya ce yake yi akan wadanda suka zabe shi a zaben fidda gwani. Amma fa tuni ya fadi manufofinsa kafin yin wancan zabe da ake dangantawa. A wasu lokuttan kuma sai ace, "muna neman goyon baya ne don azo mu tafi tare don ceto.....daga halin da ake ciki. 
A batun canjin shekar jam'iya kuwa, abu ne daɗaɗɗe wanda mafi yawan wadanda suka sha kaye a wajen zabe kan yi domin nuna fushin su da kuma korafe-korafen su wanda mafi yawan furucin da kan fito a bakunan su shi ne, "anci amanar mu, an yaudare mu, ba'a yi mana adalci ba magudi aka yi mana" da sauran lafuzza. Amma sukan manta da cewa a can baya, suna cewa, duk wanda ya ci a tsakanin su zasu goya mashi baya. A wannan karon, sabbin jini ko sabbin yanka Raken siyasa suka fi mayar da hankali akan yin wannan canjin sheka. Sun manta da cewa, duk wani hangen da suke yi musamman na abinda zasu samu tuni a n baiwa wasu shi illa ana jiran jin zabe ne. Kazalika, basu samu ƙwarewar da ta dace ba akan harkokin siyasar, sai su kwaikwayi tsaffin hannu ga harkar. Koda yake, ba za'ayi saurin yanke masu hukunci ga abinda ka iya faruwa ba a gaba, amma tabbas akwai alamun yin nadama a wajen su musamman idan akayi nasara a inda suka koma din duk kuwa da cewa, an saba a siyasa mai yi mata wahala daban mai cin moriyar daban. 
To shin kai ziyarar ɗan takara ga wani ko wasu ko kuma ziyarar wani ko wasu ga ɗan takara ko taron yin godiya gami da ƙara tallata kai da manufofi na nuni da yaƙin neman zabe ne ta wayo ko neman magoya bayan ɗan takara ko jam'iya? 

Post a Comment

Previous Post Next Post