TAƁARƁAREWAR AL'ADUN HAUSAWA A ƘARNI NA 21

Waiwaye kashi na 1 
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
"TAƁARƁAREWAR AL’ADUN HAUSAWA A ƘARNI NA 21:" 
Illolin da Suka Haifar Wajen Kawo Rashin Tsaro a Ƙasar Hausa 
                               Na
Farfesa Bashir Aliyu Sallau Sashen Koyar da Hausa Jami’ar Gwamnatin Tarayya Dutsin-ma Jihar Katsina Tarayyar Nijeriya 
Takarda da Aka Gabatar a Babban Taron Ranar Hausa ta Duniya na Shekara ta 2022 Wanda Kwamitin Shirye-Shiryen Ranar Hausa, Reshen Jihar Katsina ya Shirya a Ranar Lahadi, 28 ga Watan Agusta, 2022 , a Ɗakin Taro na Minaj, kusa da Rukunin Gidaje na Sarki Kabir Usman Ring Road, Katsina   
 GABATARWA
Cigaban kowace al’umma yana da matuƙar alaƙa da irin yadda wannan al’umma ta yi riƙo ga kyawawan al’adunta. Haka kuma, biyayya ga kyawawan al’adu na taimaka wa al’umma ta zauna lafiya da samun bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa. Al’ummomi daban-daban a wannan duniya ta yau waɗanda suka riƙe kyawawan al’adunsu na daga cikin waɗanda suke zaune lafiya da samun bunƙasar tattalin arziki. A ɗaya ɓangaren kuwa, watau al’ummomin da suka yi watsi da kyawawan al’adunsu suka ɗauki marasa kyau na daga cikin al’ummomin da suke cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi a yau.
A al’adance iyaye ne suke fara koya wa ‘ya’yansu tarbiyya mai kyau, daga baya kuma sai malaman makaranta ta Islamiyya ko ta zamani su ɗora a kan ta farko yadda yaro zai koyi halaye ingantattu, masu kyau yadda zuri’arsa da al’ummarsa za su yi alfahari da shi. Sannu a hankali sakamakon shigowar baƙi da ire-iren al’adunsu, musamman Turawa da suka kawo ilimin boko da kuma kafa manyan makarantu a sassa daban-daban na Tarayyar Nijeriya da wasu sassan Afirka, sai matasa suka fara kwaikwayon wasu munanan al’adu suka watsar da kyawawan al’adu waɗanda suka gada iyaye da kakanni. Sakamakon watsar da kyawawan al’adunmu da matasa suka yi an sami babbar ɓarna wadda ta haifar da taɓarɓarewar al’adu da rashin bin doka da rashin biyayya ga manya da sauransu, musamman a sassa daban-daban na Tarayyar Nijeriya da kuma Jamhuriyar Nijar. Dangane da haka, burin wannan takarda shi ne ta yi nazari don fito da yadda al’adun Hausawa suka taɓarɓare a Arewacin Nijeriya da kuma Kudancin Jamhuriyar Nijar dangane ire-iren illolin da wannan al’amari ya haifar wa wannan yanki a Ƙarni na 21. Sannan kuma a kawo shawarwarin da za a bi don gyara al’amarin yadda al’umma za ta zauna lafiya a sami walwala da bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa.
ƘARNI NA ASHIRIN DA ƊAYA (Ƙ21) 
A wannan takarda Ƙarni na Ashirin da Ɗaya (Ƙ21) na nufin shekara ta Dubu Biyu zuwa yau (2000-2022) lokacin da ƙasar Hausa da sauran sassan duniya suka sami wasu sauye-sauye da suka shafi yadda ake gudanar da al’amuran rayuwa na yau da kullum, musamman abubuwan da suke da dangantaka da zamantakewa. 
Waɗannan sauye-sauye sun kawo ci-gaba a wasu sassan rayuwa, kuma sun kawo sauye-sauyen da suka gurɓata rayuwar matasa da wasu manya. Daga cikin abubuwan da suka kawo waɗannan sauye-sauye akwai samuwar talabijin da wayar hannu da Yanar Gizo(Internet) da kuma fataucin miyagun ƙwayoyi waɗanda ake sha ko shaƙa a fita cikin hankali. Haka kuma, kwararowar ƙananan makamai daga ƙasashe maƙwabta da aka riƙa shigowa da su daga arewa da arewa maso gabacin ƙasar Hausa waɗanda suke iyaka da ƙasar Libya, musamman Jamhuriyyar Nijar da Chadi da Kamaru. Ire-iren waɗannan makamai ne ‘yan ta’adda da ‘yan fashi da makami suke amfani da su wajen kai wa al’ummomin ƙasar Hausa da maƙwabtansu hare-hare da kashe mutune da kuma yin garkuwa da wasu don a biya kuɗin fansa da sace dukiyoyinsu da matansu waɗanda a mafi yawancin lokuta sukan yi musu fyaɗe. Waiwaye Kan Ƙasar Hausa da Mutanenta Masana da manazarta da ɗalibai kan tarihi da al’adun Hausawa da zamantakewar Hausawa irin su Alhassan, (1981:1) da Ibrahim, (1982:1) da BirninTudu (2002:11-12) sun yi cikakkun bayanai a kan farfajiyar ƙasar Hausa. A taƙaice a iya cewa, ƙasar Hausa tana shimfiɗe a shiyyar Sudan ta Tsakiya, a tsari na gargajiya a iya cewa, ta haɗa da ƙasashen sarakunan Katsina da Kano da Daura da Zazzau (idan aka ɗebe kudancin Zazzau) da Kabin Argungu da Gwandu da Gumel da Haɗejiya a Nijeriya ta Arewa da kuma Ƙwanni da Maraɗi da Tassawa da Arawa da Gubawa a Kudancin Jamhuriyar Nijar da kuma Kangiwa da wani ɓangare na Jihar Kabi a Arewacin Nijeriya.
    Idan muka juya kan mazauna ƙasar Hausa, a iya cewa mafi yawancin mazauna ƙasar Hausa al’ummar Hausawa ne, amma akwai wasu ƙabilu waɗanda suka yi kaka-gida waɗanda a yau wasunsu sun koma Hausawa a harshe da al’ada da adabi waɗanda suka haɗa da Fulani da Buzaye da Barebare da Nufawa da Yarabawa da sauransu. Idan kuma ana maganar su wane ne Hausawa? A nan ma masana da manazarta da ɗalibai irin su Ibrahim, (1982:1) da Adamu,(1983: 3) da Magaji,(1986:3) da kuma Sallau,( 2000:71) sun bayar da gamsassun bayanai kan mutanen da ake cewa su ne Hausawa. A taƙaice a iya cewa, Hausawa dai su ne mutanen da suke magana da harshen Hausawa a matsayin harshen da suke hulɗoɗin rayuwa ta yau da kullum ko da kuwa asalinsu ba Hausawa ba ne, sakamakon zama cikin Hausawa sun rabu da harshensu da al’adunsu da adabinsu na asali suka ɗauki na Hausawa.
WAIWAYE AKAN AL'ADUN HAUSAWA
 Masana irin su Ibrahim, 1982 da Bunza, 2006: xxv, xxxii, sun gabatar da bayanai dangane da asali da ma’anar kalmar al’ada. A dunƙule kalmar al’ada tana nufin dukkanin rayuwar ɗan Adam tun daga haihuwarsa har zuwa Kabarinsa. Ta la’akari da haka, a iya cewa al’ummar Hausawa kafin shigowar Turawan Mulkin Mallaka suna da ingantaccen tsarin al’adun da suke tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum. Ire-iren waɗannan al’adu ne suke zama jagora ga kowace zuri’a dangane da abubuwan da suka dace a yi da kuma waɗanda ba su dace a yi ba. A wasu fannoni ana samun wasu wuraren da zuri’o’i suke yin haɗaka a kan wasu al’amura waɗanda suka shafi yadda suke gudanar da harkokin rayuwarsusu, musamman ta fuskar tarbiyya da aure da haihuwa da mutuwa da zamantakewa da sauransu. Daga cikin waɗannan fannoni na al’ada za a tarar mafi yawanci zuri’o’i suna koya wa ‘ya’yansu yin cikakkiyar biyayya ga abin da suke bauta da koya musu sana’o’insu na gargajiya da ƙulla danƙon zumunci da gaskiya da riƙon amana da biyayya ga shugabanci da taimakon juna da kara da nuna alkunya da sauransu.
TARBIYYA A WAJEN HAUSAWA :
Tun lokaci mai tsawo da ya gabata kafin shigowar addinin Musulunci ƙasar Hausa, al’ummar Hausawa suke gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya. Wannan kuwa ya faru ne saboda suna da kyakkyawan tsarin tarbiyya wanda ya ba kowa damar sa yadda wani ba ya shiga cikin harkar da ba ta shi ba. Wannan dalili ne ya sa ko da addinin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa, ba a fuskanci wasu manyan matsaloli ba dangane da halin zamantakewar wannan al’umma. Matuqar ana son kwalliya ta biya kuxin sabulu a tsarin zamantakewarmu ta yau, to ya dace a koma wa tsarin tarbiyyar Hausawa ta gargajiya da ta addinin Musulunci.
- Matsayin Tarbiyya Wajen Gina Ingantacciyar Al’umma 
Dukkan al’ummar da take son ta zauna lafiya, kuma ‘ya’yanta su sami ci gaba mai ɗorewa, dole ne ya zama tana da wasu ingantattun matakai na tarbiyya waɗanda za su taimaka wa wannan al’umma ta zama ta gari. Tun kafin zuwan wannan zamani al’ummar Hausawa suna da ire-iren waɗannan matakan tarbiyya waɗanda suka taimaka wa wannan al’umma ta zama ta gari abin koyi ga maƙwabta na kusa da ma na nesa. Waɗannan matakan tarbiyya sun haɗa da kiyaye dokokin addini, da biyayya ga shugabanci, da bin gaskiya da riƙon amana, da sadar da zumunci da taimakon juna da aiki tuƙuru da kara da alkunya da riƙo da sana’o’in da aka gada iyaye da kakanni don taimaka wa rayuwar yau da kullum yadda za a sami ingantacciyar rayuwa da bunƙasar tattalin arziki (Sallau, 2013:2-19).
- Dalilan da Suka Haifar da Taɓarɓarewar Al’dun Hausawa a Wannan Zamani 
Kafin zuwan wannan zamani al’ummar Hausawa na biyayya ga tsarin zaman iyali da biyayya ga shugabanci da addininsu. Haka kuma, suna taimaka wa ‘yan’uwa da abokan arziki da kara da alkunya da ƙulla danƙon zumunci da sauransu. Sakamakon watsar da waɗannan ingantattun hanyoyin tarbiyya sun haifar da taɓarɓarewar al’adun Hausawa a wannan zamani. Dangane da haka, a iya cewa rashin ingantaccen shugabanci a tsakanin al’umma na daga cikin abubuwan da suka haifar da taɓarɓarewar al’umma. Lokacin da ya gabata shugabanni na iyakar ƙoƙarinsu wajen kare mutunci da dukiyar talakawansu. Haka kuma, a ɓangaren talakawa suna yin cikakkiyar biyayya ga waɗanda suke shugabantarsu. Wannan kyakkyawar fahimta tsakanin shugabanni da talakawa ta haifar da zaman lafiya da bunƙasar tattalin arzikin ƙasar Hausa. A wannan zamani an sami babban sauyi wanda ya haifar da taɓarɓarewar shugabanci a tsakanin al’ummomin Hausawa. A wasu sassa na ƙasar Hausa an sami wasu shugabanni waɗanda suke taimaka wa ta’addanci, waɗanda sakamakon ingantaccen bincike ya bayyana suna da hannuwa dumu-dumu wajen taimaka wa ‘yan ta’adda don su riƙa samun wani abu daga gare su. Ta ɓangaren mabiya wato talakawa, al’amarin ya fi muni, don kuwa daga cikinsu ne ake samun waɗanda suke ba ‘yan ta’adda bayani na sirri (waɗanda aka fi kira da sunan infoma) kan kowane mutum da abubuwan da ya mallaka don kai masa farmaki a sace dukiyarsa ta kuɗi da dabbobi, a wasu lokuta a tafi da shi ko matansa ko danginsa ko ‘ya’yansa don a biya kuɗin fansa. Ayyukan infoma sun taimaka ƙwarai wajen cuta wa al’umma, don kuwa su ne ƙashin bayan munanan ayyukan ‘yan ta’adda. Rashin taimakon juna a wannan zamani ya taimaka matuƙar gaya wajen taɓarɓarewar al’adun Hausawa a wannan zamani, saɓanin lokacin da ya gabata da dukkan al’umma ke taimaka wa juna don kawo zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziki. A wannan zamani mafi yawan matasa sun dogara ga aikin gwamnati ko na kamfanoni, saɓanin lokacin da ya gabata da kowane gida yake aiwatar da sana’ar da suka gada. Gudanar da waɗannan sana’o’i na gargajiya sun taimaka wa al’ummar ƙasar Hausa wajen yin ayyukan yi ba tare da dogara ga wani ba.
Zamu ci gaba a kashi na 2

Post a Comment

Previous Post Next Post