Matsalar ambaliyar ruwa JAHAR KATSINA TA HAU TUDUN MUN TSIRA

Matsalar ambaliyar ruwa  JAHAR KATSINA TA HAU TUDUN MUN TSIRA
Daga Aminu Isa Babban Daraktan kafar sadarwar zamani na gwamnatin Jahar 

Binciken masana ya nuna irin yadda ambaliyar ruwa ta addabi wasu jihohin arewa a wannan shekarar musamman manyan birane da garuruwan da ke da makwabtaka da manyan hanyoyin ruwa, irin haka ya faru a Yobe, Jigawa, Kano, Zamfara da wasu sassan arewacin kasar nan da dama. 
Kafin zuwan gwamnatin Masari sanin kowa ne cewa kwaryar Katsina da wasu shiyoyinta har faduwar gaba suke in aka ce ga damuna tafe, sakamakon fargaba na ambaliyar ruwa da kuma karancin magudanan ruwa da ake fama da su a jihar. 
Daga cikin kudurorin gwamnatin Masari na farfado da jihar Katsina tun a zango na farko akwai aiki tukuru domin ganin an magance wadannan matsaloli na kwararowar hamada da ambaliyar ruwa da ke addabar jihar kusan a duk shekara. 

Aiki na farko da gwamnatin Rt. Hon Aminu Bello Masari ta maida hankali a kansa wannan bangaren ne, kuma cikin ikon Allah kwalliya ta biya kudin sabulu, in muka waiwaya baya zamu ga cewa an gudanar da ayyuka da suka hada da:
•Samar da katafariyar hanyar ruwa ta ta taso daga shataletalen kofar Kwaya zuwa shataletalan kofar Kaura Hanyar ruwa da ta tashi daga titin gidan rodi ta biyo cikin sabuwar unguwa ta ratso kofar kaura ta shigo ta cikin kwalankwalan ta fita layin zana ta shiga kofar Marusa ta bi ta unguwar Katsira ta wuce ta kofar Durbi ta bi ta filin Samji ta dire kofar Sauri.

•Hanyar ruwa da ta taso daga bayan ATC ta shigo Unwala ta bi ta ‘Yankifi ta biyo bayan shararar pipe ta tsallaka titin kofar Kaura ta bi ta tsohon gidan Surajo mai Asharalle ta wuce ta kwalankwalan ta dire a kofar Marusa.

•Hanyar ruwa ta unguwar Daki tara zuwa kwalankwalan Hanyar ruwa ta kofar guga wadda ta shiga lambobi da karade duk unguwannin da ke gefen wurin.

•Samar da manyan magudanan ruwa a unguwannin mabambanta a karamar hukumar Rimi da garuruwan Abukur da Makurda

•Samar da hanyoyin ruwa a karamar hukumar Jibiya da kewaye, Gina magudanan ruwa a karamar hukumar Malumfashi

•Samar da kananan hanyoyin ruwa a kanana hukumomin , Kusada, Zango, Mai’adua, Rimi, Batsari, Danja, Dandume, Kafur, Kaita, Bindawa sai kuma wadanda ake kan yi yanzu a kananan hukumomin Charanchi, Batagarwa, Kankara, Faskari, Matazu, Musawa da sauransu.

•Wadannan ayyuka sune suka taimaka wajen fitar da jihar Katsina daga halin ambaliyar ruwa da aka sha fama da shi a baya, ko shakka babu gwamantin Masari a wannan fage ta tserewa sa’a.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post