Masari ga mahalarta taro... KU ƘARA NAZARI AKAN HANYOYIN MAGANCE MATSALAR TSARO

Masari ga mahalarta taro..... KU ƘARA NAZARI AKAN HANYOYIN MAGANCE MATSALAR TSARO
Daga Abdulhadi Bawa  SSA, Katsina

Gwamnan Jahar Katsina Aminu Bello Masari yayi kira ga mahalarta taron da ake yi kan magance matsalar tsaro da su fadada nazari da bincike a kan hanyoyin da za abi da kuma irin matakan da za a dauka wadanda za su magance matsalar tsaron da ta addabi mafi yawancin jihohin Arewa maso yammacin kasar nan tare da Jihar Maradin Jamhuriyar Nijar.

Gwamnan yayi wannan kiran ne cikin jawabin da ya gabatar wajen bude taron wanda Gwamnan Jihar Maradi Alhaji Shu'aibu Abubakar ya kirawo ita gwamnatin jihar Katsina take daukar nauyi.

Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana irin matakan da gwamnatin shi ta dauka wajen kawo karshen wannan matsala, wanda suka hada da yin doka wadda ta kafa kwamitocin tsaro hawa ukku; matakin Maiunguwa, matakin Magaji da kuma matakin karamar hukuma wanda ya kunshi Hakimai.

Haka kuma ya bayyana irin matakan da gwamnatin take dauka na tallafa ma jami'an tsaron ta hanyoyi daban da suke kara masu karsashi wajen sauke nauyin da yake kan su na tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma.

A nashi jawabin, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto wanda kuma shi ne shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya, yayi godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari da kuma Shugaba Muhammadu Bazoum na Jamhuriyar Nijar saboda amincewa da bada goyon bayan su domin ayi wannan taro da ake sa ran zai fito da tartibiyar hanyar da za dakile wannan matsala. Ya kuma gode ma Gwamnan Jihar Maradi saboda hangen nesan shi wanda ya jaza kiran wannan, ya kuma yaba wa Gwamna Aminu Masari saboda daukar nauyin taron. 

Shi kuwa Gwamna Bello Muhammadu Matawalle na jihar Zamfara, wanda Mataimakin shi Sanata Nasiha ya wakilta, ya bayyana cewa duk da irin matakan da gwamnatin shi take dauka, a shirye suke su rungumi duk shawarwarin da wannan taro zai zartas na bai daya domin ganin an gudu tare an kuma tsira tare.

Gwamna jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu da shi ma Mataimakin shi Kanar Samaila Yombe Dabai (ritaya) ya wakilta, ya bayyana gamsuwa da kiran wannan taro tare da fatar zai haifar da da mai ido, ta yadda za a shawo kan wannan matsala.

A jawabin shi na maraba Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina wanda shi ne Mai ba Gwamna Masari Shawara a kan harkokin tsaro, ya bayyana muhimmanci tare kuma da ribar da jihohin za suci idan aka hada kai tare da daukar matakin bai daya wajen tunkarar wannan matsala da taki ci taki cinyewa. Ya kuma yaba tare da yin jinjina ga Gwamna Aminu Bello Masari saboda duk abinda ake bukata shugaba yayi a cikin irin wannan yanayi to yayi fiye da abinda ake sa rai.

Post a Comment

Previous Post Next Post